Yan gudun Hijra
'Yan gudun hijira a jihohin Niger da Borno sun roki Shugaba Bola Tinubu ya tausaya musu wurin dawo da Ministar jin kai da walwala, Dakta Betta Edu.
Wasu miyagun 'yan bindiga sun kai hari kauyen Dan Isa dake karamar hukumar Kauran Namoda a Zamfara. Sun kashe mutum hudu tare da sace wasu dari da hamsin.
Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umaru Zulum ya buɗe shirin mayar da ƴan gudun hijira zuwa gida tare da tallafa masu da kudi da kayan abinci.
Hukumomin lafiya sun fara korafi kan yawan samun haihuwar jarirai a sansanin gudun hijira a jihar Benue inda aka haifi 200 a cikin wata daya kacal.
A ranar Jumu'ah da ta gabata yan bindiga sama da 300 suka kai hari garin Kuchi da ke jihar Neja suka kama mutane da dama. Yan bindigar sun zauna a garin.
Yan bindiga sun kai hare hare a yankunan Roro, Unguwan Usman, Rumace da Bassa a karamar hukumar Shiroro. Hakan ya tilastawa mutane da dama gudu daga gidajensu.
Wata mata mai shekaru 35 ta yanke jiki ta fadi, ta kuma mutu nan take a sansanin 'yan gudun hijira da ke jihar Benue. Ta mutu ta bar yara shida har da 'yan biyu
Wani mummunan lamari ya afku a Borno ranar Talata yayin da gobara ta tashi a sansanin 'yan gudun hijira na Muna da ke yankin Muna a jihar Arewa maso Gabas.
Wasu ƴan ta'adda da ake kyautata zaton mayakan Boko Haram ke sun farmaki garin da ake sake ginawa ƴan gudun jira a karamar hukumar Dikwa ta jihar Borno.
Yan gudun Hijra
Samu kari