Kamfanin wutar lantarkin Najeriya
Dan takarar shugaban kasa a zaben 2023, Atiku Abubakar ya yi Allah wadai da rashin wutar lantarki musamman a Arewacin Najeriya inda ya ba da shawarwari.
Tushen wutar lantarkin Najeriya ya lalace sau 105 a mulkin Buhari da Bola Tinubu. Tun fara mukin Buhari aka samu lalacewar tushen wutar lantarki sau 93 a Najeriya.
Legit Hausa ta gudanar da wani ɗan bincike kan halin da mutane ke ciki saboda lalacewar wutar lantarki a wasu yankunan Arewa, masu caji dai kasuwa ta buɗe.
Kamfanin TCN ya bayyana cewa za a cigaba da samun matsalar lantarki a Arewacin Najeriya saboda matsalar tsaro. Ko an gyara wutar Arewa ba lallai ta wadata ba.
Ministan makamashi, Adebayo Adelabu ya yi magana kan sauran Ministoci da aka sallama inda ya yabawa Bola Tinubu kan daukar matakin da ya yi a gwamnatinsa.
Kamfanin TCN ya gano matsalar wutar lantarki a Arewacin Najeriya. An fara gyara wutar Arewa kuma ana tsammanin wuta za ta dawo a Arewa nan kusa kadan.
Bayan lalacewar babban layin wutar lantarki na ƙasa sau 3 a mako guda, matasa sun fara kiran a tsige ministan makamashi, Adebayo Adelabu da shugaban TCN.
Yawaitar matsalar wutar lantarki da ake samu ya kasar nan ya jawo hankalin gwamnatin kasar nan wajen gano matsalar da ta addabi bangaren wutar a kasa.
Kamfanin wutar lantarkin Najeriya (TCN) ya ce jihohin Arewa maso Gabas, Arewa maso Yamma da kuma sassan Arewa ta Tsakiya za su fuskanci daukewar wutar lantarki.
Kamfanin wutar lantarkin Najeriya
Samu kari