Kamfanin wutar lantarkin Najeriya
Kudirin lantarki ya zama doka bayan sa hannun Bola Ahmed Tinubu a yammacin Juma’a. Dokar ta haramta raba wutar lantarki tsakanin jihohi da kasa a Najeriya.
Mata sun fito zanga-zanga a jihar Rivers don nuna damuwa kan kamfanin samar da wutar lantarki na PHED da ke hanasu saduwa da mazajensu saboda zafi.
Kamfani ya bada hakuri yayin da wutar lantarki ta dauke a wasu jihohi. Hakan ya faru ne kwanaki kadan bayan gwamnatin tarayya tayi hobbasa domin ganin an yi gyara.
Ministan wutar lantarki a Najeriya, Adebayo Adelabu ya bukaci cire tallafin wutar kantarki don samar da ita yadda ya kamata ganin yadda basuka suka yi yawa.
Cif Adebayo Adelabu, Ministan Makamashi ya fada wa yan Najeriya cewa rashin isashen iskar gas ne ya janyo karancin wutar lantarki da ake fama da shi a kasar.
Gwamnatin Neja hada da gwamnatin tarayya, kamfanin wuta, kamfanonin Kainji Hydro Electric PLC da Mainstream Energy Solutions Limited ta maka a kotu.
Babbar kotun birnin tarayya Abuja ta amince da buƙatar belin tsohon ministan wutar lantarki, Olu Agunloye kan kudi Naira miliyan N50m, EFCC ce ta gurfanar da shi.
Gwamnatin Najeriya ta sanar da shirin sayar da kamfanin rarraba wutar lantarki na Kaduna (KAEDCO). Ana bin kamfanin bashin sama da naira biliyan 110.
Kungiyar kare hakkin dan Adam da wayar da kan jama'a, CHRICED ta bayyana cewa Shugaba Tinubu ya biye wa Bankin Duniya wurin kara farashin mai da wutar lantarki.
Kamfanin wutar lantarkin Najeriya
Samu kari