Jihar Plateau
Rundunar ƴan sanda ta Najeriya ta tabbatar da cewa ba za ta yi ƙasa a guiwa ba wajen kamo dukan masu hannu a kisan rayukan da aka yi a jihar Filato.
Tsohon ɗan takarar LP a zaben shugaban ƙasa na 2023, Peter Obi ya bukaci shugaba Bola Tinubu ya katse ziyarar da ya je Faransa, ya dawo gida Najeriya.
Gwamnatin jihar Filato ta kafa sababbin dokoki saboda hana kashe kashe a jihar. An hana kiwon dare da takkaita zirga zirga da babura da zirga zirgar shanu da dare.
Atiku ya zargi gwamnatin Tinubu da gazawa wajen kare rayukan al'umma wanda ya zama silar kisan mutane 54 a Filato. Ya nemi a ba jihohi damar mallakar makamai.
Gwamnan jihar Plateau, Caleb Mutfwang, ya fito ya nemi afuwar mutanen da hare-haren ta'addanci suka ritsa da su. Ya ce gwamnati da hukumomin tsaro sun gaza.
Bincike ya bayyana cewa akwai sabani a adadin mutanen da ake ruwaito wa cewa 'yan ta'adda sun kashe a jihar Filato biyo bayan hare-haren daren Litinin.
Tsohon gwamnan Kano kuma jagoran NNPP na ƙasa, Dr. Rabiu Musa Kwankwaso ya yi Allah wadai da harin da ƴan bindiga suka kashe gomman mutane a Filato.
Gwamnan jihar Filato ya yi zama da sojoji, 'yan sanda da shugabannin kananan hukumomi kan kashe kashe da ake fama da shi a jihar. Ya ce za su hana kai hare hare.
Shugaba Tinubu ya bukaci Gamna Mutfwang ya kawo karshen rikicin Filato, yayin da Amnesty ta ce an kashe mutum 1,336 daga Disamba 2023 zuwa Fabrairu 2024.
Jihar Plateau
Samu kari