Jihar Ondo
Jama'ar yankin Oda a jihar Ondo sun shiga jimami bayan rasuwar babban basarake a jihar Ondo, Julius Omomo watanni 11 da hawa sarauta ya na da shekaru 83.
Jam'iyyar All Progressive Congress watau APC ta ce ita ce a kan gaɓa wajen kokarin samun nasara a zaben gwamnonin da ke tafe a jihohin Ondo da Edo.
Wasu manyan jagororin APC mai mulki a jihar Ondo sun zargi Gwamna Aiyedatiwa da buga katunan zama mamban jam'iyya na bogi domin maguɗin zaben fitar da gwani.
Binciken kwa-kwaf ya tabbatar babu gaskiya kan jita-jitar da ake yadawa cewa Betty Akeredolu, matar tsohon gwamnan Ondo, Rotimi Akeredolu ta auri kaninsa.
Shugaban jam'iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa, Alhaji Abdullahi Umar Ganduje, ya sha alwashin cewa jam'iyyar za ta lashe zaben gwamnan jihar Ondo.
Gwamna Lucky Aiyedatiwa ya bayyana cewa ba abin da yake jin tsoro yayin da ake shirin fafata zaben fitar da ɗan takara a inuwar jam'iyyar APC mai mulki.
Gwamnan jihar Ondo, Lucky Aiyedatiwa ya ce naɗin da kwmaishina ya yi na hadimai 273 naɗi ne ka girmamawa amma gwamnati ba za ta rika biyansu albashi ba.
Yayin da ake ci gaba da azumin watan Ramadan, 'yan sanda sun cafke wani malamin Musulunci, Alfa Oluwafemi Idris da sassan jikin ɗan Adam a jihar Ondo.
Hukumar zaɓe ta ƙasa mai zaman kanta (INEC) ta bayyana cewa jam'iyyun siyasa 19 sun nuna sha'awar tsayar da ƴa takara a zaben gwamnan jihar Ondo.
Jihar Ondo
Samu kari