Sarkin Kano
Mai martaba sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya faɗawa shugabannin tsaro cewa a soshiyal midiya kaɗai ake yaɗa umarnin kotun da ta ce kar a naɗa shi sarki.
Gwamnatin jihar Kano ta ce a rusa masarautu bai jawo tashin hankali a jihar ba, yan siyasa ne suka dauko sojojin haya domin tayar da hankali amma za a magance su.
Gwamnatin jihar Kano ta yi martani kan labarin dake bayyana bullar tashin hankali a jihar saboda rushe masarautu da nada sabon sarki Malam Muhammad Sanusi II.
Aminu Babba Ɗanagundi ya bayyana cewa mataimakin gwamnan Kano ya yi kuskuren zargin NSA Nuhu Ribadu da hannu a dawo da Sarki Aminu Ado Bsyero cikin Kano.
Gwamnatin jihar Kano ta hannun mataimakin gwamnan jihar ta bukaci shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu da ya fitar da Aminu Ado Bayero daga cikin Kano.
Majalisar dokokin jihar Kano ta musanta labarin da ke cewa ‘yan majalisar sun karbi cin hanci domin rushe masarautun jihar biyar da nada sabon sarki.
Magoya bayan sarakuna biyar da gwamnatin jihar Kano ta tube rawunansu sun gudanar da Sallar Al-Qunut tare da yin addu'ar Allah ya mayar da sarakunansu.
Gwamnatin Kano ta karbi takardar kotu kan dakatar da rusa masarautun Kano, Gaya, Karaye, Bichi da Rano a yau. Kwamishinan shari'a, Haruna Isa Dederi ne ya tabbatar.
Kamar yadda Sarkin Kano Muhammadu Sanusi ya yi zaman fada tare da hakimai a yau Lahadi an ce shi ma Aminu Bayero, tsohon Sarkin Kano, ya yi zaman fada a Nassarawa.
Sarkin Kano
Samu kari