Albashin ma'aikatan najeriya
Gwamnatin Tarayya ta dakatar da biyan kudaden rage radadin cire tallafi na ma'aikata dubu 35 da aka fara a watan Satumba, kungiyar NLC ta yi barazanar yajin aiki.
Tsohon gwamnan jihar Edo kuma tsohon shugaban kungiyar kwadago ta kasa (NLC), Adams Oshiomole, ya bukaci NLC ta tabbatar an biya ma'aikata karin albashin N35,000.
Fatara tana tada tsohon bashi, ‘Yan majalisan da aka yi a 1990s sun roki gwamnatin Bola Tinubu ta biya su albashi da alawus na aikin da su ka yi a baya.
A ranar Laraba, 6 ga watan Disamba, ne gwamnatin tarayya ta fara biyan albashin ma’aikata da aka rike da farko saboda akasi a tsarin biyan albashi na IPPIS.
Akalla ma'aikatan gwamnatin tarayya dubu biyu ne ba za su samu albashin watan Nuwamba ba. Hakan ya faru sakamakon samun matsala da suka yi a tsarin IPPIS.
NLC ta ce sai an duba yanayin rayuwar yau wajen yanke mafi karancin albashi. Joe Ajaero ya ce tun da Ibrahim Badamasi Babangida ya fito da tsarin SAP ake wahala.
Mafi karancin albashi a yau N30, 000 ne, zuwa Maris babu wanda za a biya wannan kudi.Gwamnati ta ce nan da 'yan watanni kadan sabon tsarin albashi zai soma aiki.
Shugaban manyan ma'aikatan Gwamnatin Tarayya, Tommy Okon ya bayyana cewa akalla ma'aikata dubu 5 za su samu matsala a albashin watan Disamba na wannan shekara.
Babban Bankin Duniya (WB) ya yi hasashen cewa akalla 'yan Najeriya miliyan 2.8 ne za su shiga kangin talauci nan da karshen shekarar 2023 zuwa 2024.
Albashin ma'aikatan najeriya
Samu kari