Kasafin Kudi
Akalla naira biliyan 1.95 gwamnatin jihar Zamfara ta ware don sake gina fadar sarakuna 18 da ke a fadin jihar, da nufin daga darajar masarautun gargajiya.
A yayin da wasu gwamnoni ke jiran rahoto daga majalisar jiharsu, tuni gwamnonin Katsina, Plateau da Delta suka sa hannu kan kasafin kudinsu har ya zama doka.
Majalisar jihar ta amince da naira biliyan 437 matsayin kasafin 2024 na jihar maimakon naira biliyan 350 da gwamna Abba Kabir Yusuf ya fara gabatar wa majalisar.
Hukumar Kula da Basuka, DMO ta bayyana cewa a yanzu haka basukan Najeriya sun kai naira tiriliyan 87.9 a karshen watan Satumbar wannan shekara da mu ke ciki.
Kwamitin kudi na majalisar dattawa ya ba rundunar 'yan sanda wa'adin awa 24 ta gurfanar da shugaban hukumar rijistar kamfanoni a gabanta kan kasafin hukumar.
Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani ya maida hankali a kan kauyuka, Kaduna za ta kashe N458bn a kasafin 2024. Mai girma Sanata Uba Sani ya kai kasafin gaban majalisa.
Kudin Najeriya; Naira sun kara daraja a kasuwar musayar kudi ta duniya biyo bayan dogon kai ruwa rana da aka yi a baya na darajar kudin kasar ta Afrika.
Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya roki majalisar dokokin tarayya da ta amince ma'aikatar FCT ta samu naira biliyan 17.2 da aka ware mata a kasafin 2024.
Ma'aikatar bunkasa ma'adanan Najeriya ta roki majalisar tarayya da ta kara mata Naira biliyan 250 a kasafin kudin 2024 da za a ba ta. A yanzu an ba ma'aikatar N24bn.
Kasafin Kudi
Samu kari