Masu Garkuwa Da Mutane
Tsohon Manjo a rundunar sojin Najeriya, Joe Ajayi ya rasa ransa a hannun masu garkuwa da mutane bayan an ba su kuɗin fansa har Naira miliyan 10 a jihar Kogi.
Wasu 'yan bindiga dauke da makamai sun sace mutane 127 bayan mummunan harin da suka kai jihar Kebbi. Sun kashe maza da mata yayin harin da suka kai.
Wasu masu zuwa coci ɗaukar karatun Littafi Mai Tsarki (Bible) sun faɗa hannun ƴan bindiga a hanyarsu ta komawa gida a Akure ta Yamma a jihar Ondo.
Rundunar 'yan sandan Najeriya ta samu nasarar ragargazar masu garkuwa da mutane a Abuja da jihar Jigawa. Jami'an tsaron sun kuma kwato makamai a hannunsu.
Sace tsohon Manjo din soja, Joe Ajayi mai shekaru 76 a Kogi ya jefa al'ummar garin Odo-Ape cikin fargaba, tare da ƙara tabbatar da matsalar tsaro a yankin.
Mutane a wasu yankuna na jihar Zamfara musamman karamar hukumar Kaura na Moda na barin gidajensu da dare su dare da safe saboda tsaron hare hare.
Hukumomi a kasar Saudiyya sun cafke wasu mata biyu da ake zargin iyalan dan bindiga Ado Aliero ne a garin Madina yayin da suka tafi aikin Hajji daga Najeriya.
DSS ta kama Sani Galadi a Sokoto yana kokarin tafiya aikin Hajji. Ana zargin Galadi da garkuwa da mutane a Zamfara, kuma yanzu haka yana hannun DSS domin bincike.
Jami'an DSS sun kama Yahaya Zango, hatsabibin mai garkuwa da mutane a sansanin alhazai na Abuja. Jama’a na tambaya: me zai faɗa wa Allah kan ta'addancinsa?
Masu Garkuwa Da Mutane
Samu kari