Manyan Labarai A Yau
Rabaran Ejike Mbakah na cocin AMEN ya yi gargadi ga Shugaban kasa Bola Tinubu da ‘yan siyasa. Ya tuna yadda ya yi hasashen yunwa a kasar shekaru biyu da suka gabata.
Bashir Ahmad, tsohon hadimin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya soki yunkurin gwamnan Kano Abba Yusuf inda ya bukaci da ya yi koyi da Babajide Sanwo-Olu.
Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bayyana shirinsa na ganawa da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu domin sanar masa da kangin da mutane ke ciki a yanzu.
Wata babbar kotun Kano ta yankewa wata matar aure, Rukayya Abubakar, hukuncin daurin rai da rai kan kishe ‘dan kishiyarta bayan ta jefa shi a cikin rijiya.
Bayanai da suka fito daga fadar gidan sarautar Ingila sun nuna cewa Sarki Charles ya kamu da cutar daji. An gano hakan ne yayin masa maganin matsalar mafitsara.
Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa ta'annati (EFCC) ta cafke wani babban fasto bisa zarginsa da laifin damfarar mabiyansa makudan kudi har N1.3bn.
Gwamnan babban bankin Najeriya, Olayemi Cardoso, ya fito ya yi magana kan dalilin kwashe wasu ofisoshin babban bankin da ga birnin Abuja zuwa Legas.
An samu asarar rayukan mutum shida a wani mummunan hatsarin mota da ya auku a jihar Ebonyi. Wasu mutum 11 sun kuma samu munanan raunuka a hatsarin.
Oba Adebayo Fatoba, babban basarake a jihar Ekiti, ya bayyana yadda ya tsira daga hannun masu garkuwa da mutanen da suka halaka takwarorinsa biyu.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari