Auren jinsi
Shugaban kungiyar lauyoyin Najeriya ta NBA, Yakubu Maikyau ya bayyana cewa kwata-kwata babu batun auren jinsi a yarjejeniyar kamar yadda wasu ke yadawa.
Bulaliyar masara rinjaye na majalisar Wakilai, Hon. Sani Madaki ya gabatar da kuduri gaban majalisar da ya nemi gwamati ta dakata daga aiwatar da yarjejeniyar Samoa
Fitaccen malamin Musulunci, Sheikh Ibrahim Masari ya yi martani kan yarjejeniyar Samoa ya ce ya kamata a rinka yin adalci ga wadanda ake so da wadanda ba a so.
Majalisar limamai da malaman Musulunci a jihar Kaduna sun yi Allah wadai da yarjejeniyar Samoa da gwamnati ta sanyawa hannu inda suka shawarci Majalisun Tarayya.
Matasa a jihar Kano sun fara barranta kansu da duk wani yunkuri na marawa auren jinsi da dangoginsa baya a kasar nan, inda su ka gudanar da zanga-zanga a yau.
Hukumar Hisbah ta nesanta kanta da gayyatar kungiyar da aka gano ta na cusa ra'ayin auren jinsi da dangoginsa 'WISE' a Kano, inda ta ce ba ta san jami'in ya je ba.
Shugaban sashen kiwon lafiya na hukumar Hisbah a Kano, Idris Ahmed ya fito ya yi karin haske kan zargin da aka yi na yana kare 'yancin masu auren jinsi.
Bayan bullar kungiyar Wise, gwamnatin jihar Kano ta ba hukumar Hisbah umarnin cafke duk wata kungiya da aka samu tana tallatawa ko rajin kare masu auren jinsi.
A yammacin Asabar din nan matasa, musamman masu fafutukar kare hakkin dan Adam a Kano su ka fara kururuwar gano wata kungiya mai yada mugun nufi a Kano.
Auren jinsi
Samu kari