Yadda wani mutumi yake samun kudi ta hanyar yin bacci
- Wani mutum mai suna Alex Shannon ya mayar da lalacin shi zuwa hanyar samun kudi
- Ya karyata wannan maganar mai cewa ba a samun kudi yayin da ake bacci
- Mutumin mai shekaru 35 na zuwa sassa daban-daban na duniya ne don nuna bajintarshi a fannin bacci, wanda hakan ke kawo mishi kudi
Wani mutum mai suna Alex Shannon ya mayar da lalacin shi zuwa hanyar samun kudi. Shannon yaje otal daban-daban a fadin duniya tare da bayyana hazakar shi ta bacci.
Dan shekaru 35 a duniyan ya kafa tarihin zama wanda ke jan hankalin mutane a kan bacci, na farko a duniya.
Dan asalin London din ya karyata wannan karin maganar mai cewa kudi baya zuwa idan ana bacci.
KU KARANTA: Nayi aure ne a kasar Thailand shine yasa na bar Kannywood - Rashida Labbo
Mutumin na samun kudin shi ne ta hanyar yin bacci. Yana zagaye duniya tare da nuna hazakar shi ta bacci ga mutane a manyan otal da ke duniya tare da wallafawa a shafukan sada zumuntar zamani.
Shannon ya ce wannan dabarar tazo mishi ne a yayin da yake bacci kuma a cikin mafarki.
Ya samu damar zuwa otal a Amurka, Dubai da Paris. Ya ziyarci wurare masu tarin yawa a duniya kuma bashi da niyyar dainawa.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng