Labaran Duniya
Mutane shida sun mutu a wajen cunkoson daukar aikin sojoji a Accra, Ghana. Gwamnati ta dakatar da shirin kuma Shugaba Mahama ya ziyarci wadanda suka ji rauni.
Fasto Enoch Adeboye ya roƙi Shugaba Bola Tinubu da ya nemi sulhu ta diflomasiyya da Amurka kan barazanar harin soja da Donald Trump ya yi mata a wannan wata.
Koriya ta Arewa ta yi barazanar ɗaukar matakin kai hari yayin da jirgin yakin Amurka ya isa Koriya Ta Kudu. Ta zargi Amurka da hada baki da Koriya ta Kudu.
A tarihi, Amurka ta dauki matakin soji na kai faramaki a kasashe da dama da nufin yakar yan ta'adda da ke kashe fararen hula, daga ciki kawai Libya da Iraq.
Wani bako ya fadi a lokacin wani taro da Shugaba Donald Trump ya jagoranta a Fadar White House, yayin da ake magana kan rage farashin maganin kiba.
Yan Majalisar Dokokin Amurka 31 sun bayyana Shugaba Trump a matsayin jarumi bisa sanya Najeriya a jerin kasashen da ake da babbar matsala kan yancin addini.
Wata kotun Ingila ta yanke hukuncin cewa yaron da ya kai iarar iyayensa ya ci gaba da zama a Ghana har sai ya kammata karatu ya yi jarabawar GCSE.
Hukumomi sun tabbatar da mutuwar mutane tara yayin jirgin sama na dakon kaya ya rikito kan masana'antu a kasar Amurka, ana ci gaba da aikin ceto mutane.
Donald Trump ya ba da umarnin a fara gwajin makaman nukiliya nan da nan don daidaita da Rasha da China, matakin da ya haifar da suka daga majalisar Amurka.
Labaran Duniya
Samu kari