Zaben jihohi
Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta ki sauraron karar da yar takarar APC a zaben gwamnan jihar Adamawa, Sanata Aisha Dahiru Binani ta shigar a gabanta.
Rahotanni sun bayyana kan ranar da hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) za ta bayyana sakamakon zaɓen gwamnan jihar Adamawa mai cike da umbin ruɗani.
Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, ya roki hukumar zabe mai zaman kanta ta ƙasa ta gaggauta gyara kuskuren da jami'inta ya tafka a zaben gwamnan jihar Adamawa.
Aisha Dahiru Binani ta kai kara domin Kotu tayi umarnin dakatar da zaben Adamawa, Lauyan ta ya ce INEC ta shiga lamarin da ya fi karfinta da ta soke sanarwa.
Jam'iyyar PDP mai mulki a jihar Adamawa ta shiga zanga-zangar nuna adawa da. sakamakon zaɓen gwamnan jihar. Jam'iyyar tace za ta ci gaba har sai baba ta gani.
Mutanen Imo sun samu wakilcin matashi kamar yadda aka samu a Kebbi da Sokoto. Wanda zai zama sabon ‘Dan majalisar mazabar Mbaitoli/Ikeduru, dan kasa da 30 ne.
Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa INEC ta umarci REC ɗin jihar Adamawa da ya nesanta kansa daga duk wasu harkokin zaɓen jihar bayan abinda ya aikata jiya.
An shiga cikin ruɗani a Adamawa kan sakamakon zaɓen cike gurbi na gwamnan jihar na ranar Asabar. Mun yi duba kan wasu abubuwan sani dangane da halin da ake ciki
Wasu mutane da ba a san ko su wanene ba a jihar Adamawa sun yi wa wani kwamishinan hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) wanda aka boye sunansa zigidir.
Zaben jihohi
Samu kari