
Kiwon Lafiya







Gwamnatin tarayya ta nemi sabon bashin dala miliyan 300 daga Bankin Duniya don inganta kiwon lafiya, NCDC ce za ta aiwatar da shirin a shekarar 2026.

Shugaba Tinubu ya amince da daukar likitoci 50 da malaman jinya 100 don kula da lafiyar fursunoni, tare da gyaran gidan yarin Kuje da sabbin wuraren kiwon lafiya.

Dakta Sam Adegboye ya musanta cewa yawan jima’i na rage hadarin sankarar maraina, yana mai bada shawarar gwajin PSA don tabbatar da lafiyar maraina.

Tsohon dan takarar shugaban kasa, Atiku Abubakar ya nemi gwamnatin APC ta tabbatar da cewa ta bayyana yadda ake kashe kudin da aka ware wa fannin lafiya.

Gwamnan Francis Nwifuru na jihar Ebonyi ya dawo da kwamishinoni guda uku da aka dakatar, ciki har da na Kananan Hukumomi, Lafiya, da Albarkatun Ruwa.

Dakatar da ayyukan USAID ya kawo cikas ga rarraba kayan tazarar haihuwa a Bauchi, amma gwamnatin jihar ta ware N50m don tallafawa UNFPA wajen samar da kayayyakin.

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ya amince da yin kari a shekarun da likitoci da sauran ma'aikatan lafiya suke yi suna aiki. Za su samu karin shekara biyar.

FEC ta ware N4.5b don sayen maganin HIV. Ministan Lafiya ya ce hakan zai tabbatar da cewa babu mai rasa magani yayin da kasar Amurka ta janye tallafi.

Masarautar Zazzau ta yi rashin jigo a cikinta, Sarkin Yakin Zazzau, Alhaji Rilwanu Yahaya Pate wanda ya koma ga mahaliccinsa a safiyar ranar Alhamis.
Kiwon Lafiya
Samu kari