Labaran garkuwa da mutane
Wasu miyagun yan bindiga sun yi garkuwa da kanana yara mata guda biyu yayin da suka kutsa kai ta tsiya cikin wani gida a babban birnin tarayya Abuja.
An sace ‘yan makarantar Apostolic Faith Group a Ekiti. Idan ana son ganin wadannan mutane, ‘yan bindigan sun bukaci a tanadi N100m a matsayin kudin fansa.
Rundunar ‘yan sandan jihar Ogun ta kama wani ma’aikacin banki, Olumide Openaike wanda ya yi karyar masu garkuwa da mutane sun sace shi saboda bashin N1.7m.
Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radɗa ya tallafawa mutanen da sojoji suka kubutar daga hannun masu garkuwa da mutane domin su koma gida da ƙarfi.
Masu garkuwa da suka sace wata likitar ido, Ganiya Olawale-Popoola da mijinta Nuruddeen Popola da wani karamin yaro Folaranmi sun nemi naira miliyan 100 kudin fansa.
Shahararren mawakin nan na Najeriya Seun Kuti, ya yi kakkausar suka ga rundunar ‘yan sandan Najeriya in da ya ya zarge su da jagorantar kungiyoyin garkuwa da mutane.
Sojoji sun kashe ‘yan ta’adda 30 da ke kan babura a karamar hukumar Birnin Gwari. Wani hobbasa da jami'an tsaro suka yi ya kubutar da wasu daga hannun 'yan garkuwa.
Adadin wadanda aka yi garkuwa da su daga 2019 zuwa yau ya kai 17, 469 Rahoto ya nuna ana da labarin rayuka kusan 2, 500 da aka rasa a karkashin Bola Tinubu.
Rundunar sojin saman Nigeriya ta yi luguden wuta kan 'yan bindiga a karamar hukumar Birnin Gwari da ke jihar Kaduna inda suka hallaka 30 a kan babura guda 15.
Labaran garkuwa da mutane
Samu kari