Labaran garkuwa da mutane
Rundunar yan sanda a birnin tarayya Abuja ta yi nasara kan gungun barayi masu garkuwa da mutane tare da kubutar da wadanda aka yi garkuwa da su a dazuka.
Rahotanni sun bayyana cewa wasu gungun 'yan bindiga sun shiga rukunin gidajen malaman majami'ar St. Thomas Parish da ke Kaduna, sun yi awon gaba da Rabaran Gabriel.
Shugaban kwamitin majalisar dattawa kan sojoji, Sanata Abdul'aziz Musa Yar'adua ya bukaci 'yan Najeriya da su daina ba da kudaden fansa ga 'yan bindiga.
Yan bindiga sun kai hari jihohin Zamfara da Katsina inda suka kashe mutane kimanin 50. Kwamishinan yan sandan jihar Zamfara ya tabbatar da faruwar lamarin.
Yadda wasu direbobin kasar nan ke awon gaba da wasu jami'an tsaro idan an tsare su a hanya ya fara ci wa rundunar 'yan sandan kasar nan tuwo a kwarya.
Rundunar yan sandan Kano ta cafke wasu mutane 19 da ake zargi da aikata mugayen laifuka iri daban-daban a jihar, ciki har da fashi da makami da satar mutane.
Gwamnatin jihar Niger ta dora laifin gaza ceto wadanda suka makale a karkashin mahakar ma'adanai kan rashin tsaro da ya addabi yankin Galadima-Kogo.
Wasu yan ta'adda sun shiga kauyuka biyu a kananan hukumomin Nunya da Tunga, sun yi awon gaba da Bayin Allah akalla 56 a jihar Neja cikin kwanaki biyu.
Rindunar sojojin Najeriya ta bayyana cewa dakarun soji sun ragargaji ƴan ta'adda a wani samame da suka kai maɓoyarsu a jihar Benuwai, sun kuɓutar da mutane da dama.
Labaran garkuwa da mutane
Samu kari