Karatun Ilimi
Gwamnatin Ondo ta ware N634m don biyan kudin WASSCE na 2024/2025 ga dalibai sama da 23,000, da nufin ba 'ya'yan talakawa damar yin karatu ba tare da matsala ba.
Gwamnatin Bauchi ta sanar da rufe dukkanin makarantu na gwamnati da na masu zaman kansu daga 1 ga Maris har zuwa 5 ga Afrilu, domin shirin azumin Ramadan na 2025.
Yayin da take kokarin inganta ilimi a shiyyar Bauchi ta Kudu, Gidauniyar Ibrahim Ali Usman ta raba fom na JAMB guda 300 ga dalibai da aka zaba daga yankin.
Gwamnatin jihar Kano za ta dauki nauyin dalibai 1,002 don karatu a kasashen waje, domin bunkasa ilimi da bai wa matasa damar gogayya a matakin duniya.
Gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta kara jaddada rashin jin dadin yadda ta gaji bangaren ilimi a cikin mummunan hali, ta dauki matakin gina sababbin makarantu.
Shugaban karamar hukumar Kumbotso, a jihar Kano, ya dauki nauyin dalibai 1,100, ya kaddamar da gyaran makarantu, rabon kayan karatu, da tallafawa matasa.
Daliba daya ta rasu, biyar sun jikkata sakamakon rushewar bangon aji a GGSS Potiskum, Yobe. Gwamnatin jihar ta ce za a binciki musabbabin hatsarin.
Gwamnatin Kano karkashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta ware N33.45bn domin gudanar da wasu muhimman ayyukan ci gaba ga al'umma a faɗin jihar.
Gwamnati Neja ta gudanar da jarrabawa ga dalibai da ake shirin turasu karatu kasashen waje. Za a tura dalibai 1,000 zuwa kasashen Canada, China, India da Brazil.
Karatun Ilimi
Samu kari