Karatun Ilimi
A ranar Laraba, majalisar dattawa ta gabatar da kudurin hukuncin dauri na watanni 6 ga iyayen da suka yi watsi da ƴaƴansu tare da ƙin tura su makarantar boko.
Shugaban Jami'ar Madonna, Rabaran Emmanuel Edeh ya bayyana cewa a makarantar ce kadai 'yan mata ke kammala karatu tare da budurcinsu saboda tarbiyar da suke bayarwa.
Jami'ar Cape Town ta ci gaba da zama babbar jami'a a Nahiyar Afrika a cikin kuma mai matsayi a jami'o'in duniya na bana kamar yadda Edu Rank ya wallafa.
Yayin da ake shan fama a Najeriya, daliban firamare da sakandare a jihar Ogun sun samu kyautar N10,000 ga kowannensu domin rage radadin da ake ciki.
Kungiya ta hada-kai an bugawa Musulman kurame Al-Kur’ani domin suyi addinin musulunci. Kurame da ke da matsalar ji sun samu damar karatun littafi mai tsarki.
Gwamnatin tarayya karkashin jagorancin Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ta tabbatar da kaddamar da shirin ba dalibai rancen kudi a wannan watan na Maris.
Rundunar ‘yan sandan jihar Yobe ta kama Mista Adamu Garba Hudu, malami a kwalejin kimiyya da fasaha ta Al-Ma’arif da ke Potiskum kan laifin lalata da dalibai.
Gwamnatin jihar Kano ta gargadi jami’an SSO da aka dauka don kula da ingancin ilimi a jihar kan kula da ayyukansu inda aka musu barazana kan alawus.
Jami’an hukumar EFCC a shiyyar Ilorin sun kama dalibai 48 na jami’ar jihar Kwara a kan wasu laifukan da suka shafi zamba ta Intanet da aka fi sani da “yahoo-yahoo.”
Karatun Ilimi
Samu kari