Nade-naden gwamnati
Abubakar Malami ne ministan shari'an da ya fi jimawa a kan mulkin tun shekarar 1999, mun haɗa muku baki ɗaya ministocin shari'a da aka yi a jamhuriya ta huɗu.
Gwamnan jihar Neja, Umaru Mohammed Bago ya sha caccaka a wurin masu amfani da kafafen sadarwa biyo bayan naɗin hadimai mata 131 da ya yi a ƙarshen makon nan.
Nasir El-Rufai ya tsokano rikici a APC da ya bada sunan wanda yake so ya maye gurbinsa a Ministoci, wasu sun ce bai dace El-Rufai ya tsaida wanda yake so ba.
A wani bidiyo da ya yadu, Lola Ade-John, sabuwar ministar yawon bude ido ta sanya hannu a takardar kama aiki sannan ta duka ta gaishe da shugaba Bola Tinubu.
Sabon ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike ya tada hankalin jama’a da ya fadi manufofinsa, zai fatataki ‘yan kasuwa da masu acaba da keke napep.
Shugaba Tinubu ya bukaci ministocinsa 45 da su yi wa kasar aiki cikin mutunci sannan su aiwatar da ayyukan da aka ba su ba wai ga jihohi ko yankunansu kadai ba.
Sabon ministan birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike ya bayyana adadin gwamnonin PDP da suka gabatarwa Shugaban kasa Bola Tinubu sunayen mutane don nada su mukamai.
Tsohon gwamnan jihar Rivers kuma ministan Abuja, Nyesom Wike ya ce sai da ya rubuta wasika ga shugaban jam'iyyar PDP da masu ruwa da tsaki kafin karbar mukami.
David Umahi da Ibrahim Geidam Sanatoci ne amma su ka hakura da aikin majalisa. Kafin nada shi ministan noma da samar da abinci, Abubakar Kyari ya je majalisa.
Nade-naden gwamnati
Samu kari