Nade-naden gwamnati
Gwamnan jihar Akwa Ibom, Fasto Umo Eno ya rusa majalisar zartarwa, ya gode masu bisa gudummuwar da suka bayar fun farko, ya ce sun ba yi bakin kokarinsu.
Shugaban karamar hukumar Obio-Akpor a jihar Rivers, Hon. Chijioke Ihunwo ya nada hadimai na musamman guda 130 watanni shida bayan nada wasu 100 da ya yi.
Gwamna jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya sayawa Hajiya Hauwa Muhammad gidan N19m, ya gyara shi da N1m don saka mata kan ƙoƙarinta wajen ci gaban jihar.
Gwamnatin jihar Kano ta fada a cikin alhini bayan daya daga cikin hadiman gwamna Abba Kabir Yusuf, Injiniya Ahmad Ishaq Bunkure ya koma ga Allah SWT a ranar Laraba.
Gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Abdulkadir Mohammed, ya dawo da wasu daga cikin kwamishinonin da ya kora cikin gwamnati. Ya nada su mashawarta na musamman.
Hukumar shirya jarrabawar JAMB da UTME ta bayyana yadda ta samu tattaro N9,013,068,510.69 daga daliban kasar nan, inda aka tura akalla Naira biliyan 6 zuwa gwamnati.
Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi ya sallami wasu daga cikin kwamishinoninsa domin inganta shugabanci da tabbatar da nagartaccen aiki ga al'umma.
Gwamnan Dikko Umaru Radda na Jihar Katsina, ya yi sauye-sauye a majalisar zartarwa don inganta manufofin gwamnatinsa inda ya ba sabon kwamishina ma'aikata.
Gwamna Zulum ya rattaba hannu kan kasafin N615.857bn. Ya yaba wa majalisar dokoki, kuma ya sanar da nadin Dr. Mallumbe a matsayin mataimakin shugaban ma’aikata.
Nade-naden gwamnati
Samu kari