Aikin noma
Gwamnatin tarayta ta kaddamar da shirin karfafa mata a fannonin noma da kiwo a Najeriya, za a taimakawa mata akalla miliyan 10 a fadin jihohin Najeriya.
Gwamnati tarayya ta sanar da shirin daukar bayanan manoma da ya hada da sunayen su domin cire masu karbar tallafin bogi. Hakan zai taimaka wajen samar da abinci.
A labarin nan, za a ji cewa tsohon hadimin marigayi Muhammadu Buhari, Bashir Ahmad ya ba matakin rage harajin shigo da abinci zuwa kasar nan kariya.
NiMet ta fitar da hasashen ruwan sama a faɗin Najeriya ranar Alhamis, tana gargadin jama'a kan ambaliya da iska mai ƙarfi. Jihohin da abin ya shafa sun hada da Kano.
Gwamnatin Neja ta yi hadaka da Aliko Dangote domin bunkasa noman shinkafa a jihar. Za a tallafawa manoma da samar da ayyuka 50,000 a jihar da kasa baki daya.
Gwamnatin tarayya ta fara shirin samar da ayyuka wa matasa har miliyan 1 a jihohi 22 da birnin tarayya Abuja ta hanyar noman waken suya, za a samar da N3.9tn.
Ambaliya ta lalata gonakin shinkafa a garuruwa 7 na jihar Kebbi, inda dubban manoma suka yi asara yayin da ake fargabar samun karancin abinci a ƙasar.
A labarin nan, za a ji cewa kungiyar bayar da agaji ta ICRC ta bayya fargaba kan halin yunwa da kananan yara da mata ke fuskanta a Arewa maso Gabas.
Manoma sun fara ajiye noma masara da sauran abubuwand suke bukatar taki saboda tashin farashi. Ana fargabar hakan zai iya haifar da karancin abinci a Najeriya.
Aikin noma
Samu kari