Aikin noma
Al'ummar jihar Kwara da dama na nuna farin cikinsu yayin da buhun shinkafa mai nauyin kilogiram 50 ya koma N52,000 zuwa N54,000 daga N80,000 da aka sayar a baya.
An fara samun saukar farashin shinkafa a kasuwannin Arewa cikin sati nan. 'Yan kasuwa da manoma sun jingina saukin da wadatar shinkafar nomar rani da saukar dala
Gwamnatin tarayya ta kaddamar da shirin noma ga mata a Arewa ta tsakiya, inda ta raba naira miliyan goma ga jihohin domin rabawa ga mata ashirin a jihohin
Gwamnatin shugaban kasa Bola Tinubu, ta karbo aron ¥15bn daga wata hukumar ƙasaar waje domin bunkasa harkar noma a Najeriya, sai an shekara 30 ba a gama biya ba.
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ya bukaci gwamnonin jihohin kasar nan da su samar da filayen kiwo ga makiyaya don kawo karshen rikicinsu da manoma.
Majalisar wakilai ta ce rashin tsaro da aka dade ana fama da shi a yankin Arewa maso Gabas da sauran sassan Najeriya ya jawo karancin samar da abinci a kasar.
An gano fasa kwauri da ambaliya a matsayin musabbabin karancin abinci da tsadar rayuwa. Wannan dai na fitowa daga gwamnatin Najeriya ta bakin ministan noma.
Jama’an gari sun sace abinci da aka tarwatsa wurin ajiyan kaya a birnin Abuja. Bisa dukkan alamu jami’an tsaro ba su ankara da wuri ba ko kuwa ba a iya kai dauki ba.
Yayin da ake shan fama da tsadar abinci a Najeriya, Gwamnatin Tarayya ta yi magana kan lokacin da za ta fara rabon kayan hatsi na tan dubu 42 a jihar Neja
Aikin noma
Samu kari