Yan bindiga
Sheikh Adam Muhammad Albaniy Gombe ya goyi bayan tattaunawa da Bello Turji, yana yaba wa kokarin Malam Musa Assadus Sunnah wajen rage kashe-kashen jama'a.
Majiyoyin da muke da su sun tabbatar da cewa yan bindiga sun hallaka wasu masallata sannan suka yi garkuwa da mutane da dama, suka tafi da su cikin daji.
Jami'an tsaro sun samu nasarar hallaka 'yan bindiga a jihar Bauchi. Jami'an wadanda suka hada har da 'yan sa-kai sun kuma kwato makamai a hannun miyagun.
Akalla 'yan bindiga 200 dauke da mugayen makamai ne suka kashe dan sanda a Babanla da ke Kwara, tare da fasa kasuwa. Sannan a suka kashe wani dan sanda a Benue.
Wasu miyagun 'yan bindiga sun sace fasinjoji bayan sun tare a kan hanya a jihar Kogi. 'Yan bindigan sun yi kwanton bauna ne a kan titi domin yin awon gaba da su.
Rundunar 'yan sandan Najeriya ta yi nasarar kama wani boka da ake zargi yana ba 'yan bindiga masu fashi da makami maganin bindiga a jihar Akwa Ibom ranar Juma'a.
Rahotanni sun tabbatar da cewa wasu yan bindiga sun kai hari kauyukan Suwa da Ding’ak a Mushere, Bokkos a Plateau, inda suka kashe mutum uku ciki har da Fasto.
Wasu rahotanni sun ce ana zargin wani kwamandan Bello Turji da ake kira Duna Sani da kisan mutane da dama, yanke kan mata da cin zarafin mata da munanan laifuffuka.
Sojojin saman Najeriya sun yi nasarar dakile harin ‘yan ta’adda a garin Rann da ke Borno, tare da hallaka sama da 30 a wani samame na daban da aka kai a Zamfara.
Yan bindiga
Samu kari