Yan bindiga
Babban hafsan sojojin saman Najeriya, Air Marshal Sunday Aneke, ya sha alwashin kwato dukkanin wuraren da ke hannun 'yan ta'adda. Ya ce ba za su yi kasa a gwiwa ba.
Wasu 'yan bindiga dauke da makamai sun kai hare-hare a jihar Neja inda suka tafka ta'asa. Miyagun sun hallaka 'yan sa-kai tare da yin awon gaba da mutane da dama.
Sojoji sun kama wani mai safarar makamai a Taraba tare da AK-47 da harsasai 53, yayin da rundunar soji ta ce za ta ci gaba da murkushe masu laifi da inganta tsaro.
Gwamnan jihar Neja, Umaru Bago ya nemi a kafa sansanonin soja a iyakokin jihar Neja domin hana 'yan bindiga shiga jihar. Ya ce zai ba da matasa 25,000 su shiga soja.
Fadar shugaban kasa ta ce rikicin Arewa ta Tsakiya ya samo asali daga mallakar ƙasa, ta’addanci da satar ma’adinai, yayin da Tinubu ke ƙarfafa zaman lafiya.
Am gudanar da wata zanga-zanga a wasu kauyukan jihar Katsina kan matsalar rashin tsaro. Mutanen dai sun fita kan tituna ne bayan hare-haren 'yan bindiga.
Bayan matsin lamba a Katsina, rashin matakan tsaro mai karfi a Kano da sulhu da 'yan ta'adda na cikin dalilai 3 da ke sa 'yan bindiga kara kaimi wajen kai hari Kano.
‘Yan bindiga sun sace daraktoci shida na ma’aikatar tsaron ƙasa yayin da suke tafiya daga Lagos zuwa Abuja domin jarabawar karin matsayin aikinsu.
‘Yan bindiga sun tare fasinjoji a hanyar Ayere–Kabba, jihar Kogi, inda suka kashe mutum ɗaya, suka sace wasu, yayin da gwamnati ke cewa tsaro ya inganta da 81%.
Yan bindiga
Samu kari