Yan bindiga
Sanata mai wakiltar Kebbi ta Kudu, Sanata Garba Maidoki, ya koka kan matsalar rashin tsaro. Sanatan ya bayyana cewa dakarun sojojin da ake da su sun yi kadan.
Yaran Bello Turji da suka kama dan bindiga Abdu Lankai da ke jagorantar sulhu a Katsina. Ya yi jawabi wa daruruwan mutane a karamar hukumar Jibia bayan an sako shi.
'Yan bindiga sun kashe mutum 50 a Katsina da Kwara; mutum 20 sun mutu a Faskari, 10 kuma a Kaiama. An kona gidaje da motoci a hare-haren da aka kai makon nan.
'Yan bindiga kusan 200 sun kashe mutum fiye da 35 a Woro, Jihar Kwara; sun kona fadar Sarki da shaguna yayin da har yanzu ba a san inda basaraken yake ba.
'Yan bindiga sun kashe mutum 10 tare da ƙona gidaje a garuruwan Woro da Nuku dake Jihar Kwara a ranar Talata; Gwamna Abdulrazaq ya yi Allah-wadai da harin.
Gwamnatin Kogi ta rufe makarantu na gaggawa har zuwa 16 ga Fabrairu, 2026; Kwamishina Fanwo ya ce an dauki matakin ne domin tsaro da kare rayukan dalibai a jihar.
'Yan bindiga sun kashe mata mai juna biyu da ɗan uwanta a Pindiga, Gombe; ƴan sanda sun kashe mahara 3 tare da ceto mutane 2 daga hannun masu garkuwa.
Sama da mutane 6,000 ne suka tsere daga gidajensu sakamakon hare-haren 'yan bindiga a garuruwan masarautar Pindiga, jihar Gombe; an tabbatar da mutuwar mutane 3.
Dakarun sojojin Najeriya sun samu nasara kan 'yan bindigan da suka addabi mutane a jihar Sokoto. Sojojin sun samu nasarar dakile wani hari da suka kawo.
Yan bindiga
Samu kari