Yan bindiga
Wasu rahotanni sun ce hare-haren sojoji a Danjibga da wasu dazukan Kudancin Zamfara na tilasta wa 'yan bindigar guduwa daga maboyarsu a Zamfara zuwa Sokoto.
An samu barkewar mummunan fada a tsakanin wasu 'yan bindiga masu gaba da junansu a jihar Kaduna. Rikicin ya yi sanadiyyar kashe miyagun 'ƴan bindiga guda 10.
'Yan bindiga na ci gaba da kai hare-haren ramuwar gayya kan kisan manyan jahororinsu da jami'an tsaro suka yi a Zamfara. Sun yi awon gaba da mutane masu yawa.
Gwamnan jihar Plateau, Caleb Mutfwang, ya nuna alhininsa kan kashe-kashen da ake yi a jihar. Ya ce masu kai.hare-haren akwai daukar nauyinsu domin su yi ta'asa.
Dakarun rundunar 'yan sanda sun ceto mata 5 a Kankara da wasu 2 a Malumfashi da ke jihar Katsina bayan fafatawa da ‘yan bindiga, an mayar da su gida lafiya lau.
Mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu, ya bukaci iyalan da mutanen da 'yan bindiga suka sace kan su daina biyan kudaden fansa.
Wasu 'yan bindiga sun kai hari kan daliban jami'ar jihar Kebbi da suka kai musu hari cikin dare suna kwanciyar zafi. An harbe wani mutum da ya fito a lokacin harin.
Wasu miyagun 'yan bindiga dauke da makamai sun kai harin ta'addanci a jihar Katsina. 'Yan bindigan sun hallaka mutane hudu tare da yin awon gaba da wasu da dama.
Gwamnatin jihar Sokoto karkashin jagorancin Gwamna Ahmed Aliyu ta koka kan yadda wasu ke kokarin kawo cikas ga shirin samar da tsaro. Ta yi gargadi kan hakan.
Yan bindiga
Samu kari