Aiki a Najeriya
Bincike ya fallasa yadda gwamnatocin jihohin kasar nan 30 suka kashe makudan kudi wajen sayen kayan kwalam da makulashe da walwalar jami'an zaman gwamnati.
Gwamnatin Gombe za ta kashe naira biliyan 20 kan gina titi mai tsawon kilomita 18.5 a ciki da wajen kwaryar jihar. Kwamishinan ayyuka na jihar ne ya sanar da haka.
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana babban titin da gwamnatinsa ke ginawa daga Lagos-zuwa Calabar da alamar ci gaba ce da zai samar da aikin yi.
An kama wasu matasa a jihar Neja bisa zargin sace fankoki a masallaci, inda aka kama wani kuma da laifin datse hannun wani dan acaba da kuma sace babur.
Gwamnatin tarayya za ta kaddamar da tashar tsandauri a Funtua dake jihar Katsina gobe Alhamis, wanda zai zama tasha irinta ta uku a Arewacin Najeriya.
Gwamnatin jihar Kano ta ce ba gaskiya ba ne cewa za ta kori masu sharar da gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje ta dauka aiki kamar yadda wasu ke yadawa.
Gwamnatin jihar Kano ta kaddamar da ginin titin dan Agundi mai hawa uku domin rage cunkoson ababen hawa. Kamfanin CCG Nigeria Limited ne zai yi aikin kan ₦15bn.
Mazauna unguwar Gwagwarwa dake jihar Kano sun zargi wani sojan Sama, Aminu Oga da kashe matashi mai shekaru 23, Yusuf Shu'aibu.Sun nemi hukumomi su bi musu hakkinsu.
Shugaban kungiyar NLC a jihar Borno, Yusuf Inuwa, ya ce kudaden fansho na Naira 4,000 da ake biya a duk wata ga wasu da suka yi ritaya a jihar ya yi kadan.
Aiki a Najeriya
Samu kari