Zaben Najeriya
An Shirya gudanar da babban zaɓen shugaban ƙasa a ranar Asabar a Najeriya. Akwai jerin jihohin da ake hasashen manyan ƴan takara 4 za su lashe babu ko tantama.
Hukumar kula da shige da fice na Najeriya ta bada umurnin rufe dukkan iyakokin kasar domin shirin babban zaben kasar da za a yi a ranar Asabar 25 ga Fabrairu.
Jihohin da suka yi zarra da sakaci wajen yawan mutanen da suka karbi katin zabe daga INEC, kason wadanda ba su karbi PVC da Hukumar INEC ta buga ba su kai 7% ba
Shugaban Amurka Joe Biden ya mika sako ga yan Najeriya, ya ce sun cancanci su zabi wanda zai jagorance su, ya kuma yabi yan takara kan yarjejeniyar zaman lafiya
Hukumar zaɓe mai zaman kanta (INEC) ta saki adadin yawan masu da za su kaɗa ƙuri'a zaɓen Najeriya. INEC ta fitar da adadin ne ana saura kwana biyu a fara zaɓe.
Yan sandan farin kaya na DSS sun kai sumame wani gida da ake amfani da shi a matsayin ofishin kamfe inda suka gano bindigu, wukake da wasu muggan makamai a Kano
Yayin da ake shirye-shiryen shiga lokacin babban zaben Najeriya, wani mafarauci ya bankado tulin dubban katunan zabe da aka boye cikin jaka a jejin Anambra.
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bukaci ’yan takarar da za su fafata a dukkan matakai da su garzaya kotu idan basu gamsu da sakamakon zaben hukumar INEC ba.
A ranar Asabar 25 ga watan Fabrairun shekarar 2023 ne ake fatan yin zaben shugaban kasa da na yan majalisar tarayya a Najeriya, da bvas za a tantance masu zabe.
Zaben Najeriya
Samu kari