Matsin tattalin arziki
Bankin duniya ya fitar da rahoto kan yadda talauci zai yi wa 'yan Najeriya katutu zuwa 2027. Bankin duniya ya ce 'yan Najeriya da dama za su kara talaucewa.
Fasto Tunde Bakare ya shawarci Shugaba Tinubu ya rungumi tawali’u da karɓar shawara domin ceto Najeriya daga halin da take ciki inda ya ce an gaji da addu'a.
Hukumar kididdiga ta ƙasa watau NBS ta bayyana cewa an samu ƙarin hauhawar farashin kayayyaki daga 23.18% a watan Fabrairu zuwa 24.23% a watan Maris, 2025.
China ta kara haraji kan kayayyakin Amurka zuwa 125% yayin da rikicin kasuwanci ya kara kamari. China ta ce ta shirya yin karar Amurka gaban hukumar WTO.
A kasuwar hatsi ta Potiskum da ke jihar Yobe, wake ya yi tashin gwauron zabi yayin da farashin masara, dawa da gero suka sauka. Ana sayar da shinkafa kan N51,000.
Gwamnatin Nasarawa ta ci gaba da tallafawa talakawa 6,000 da N7,000 a kowanne wata. An ce shirin zai karfafa dogaro da kai da kuma habaka sana’o’in hannu.
Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023, Peter Obi ya nuna damuwa kan yadda abubuwa suka tabarbare a Najeriya. Ya ce mutane na kara talaucewa a kullum.
Gwamnatin Bola Tinubu za ta samar da shirin tallafin N300bn ga mutanen da suka gama karatu ba su samu sana'a ba. kowane mutum daya zai iya samun N10m.
Farashin abinci kamar shinkafa, doya, wake da gyada na ci gaba da sauka a Najeriya, wanda ya faranta ran magidanta da iyalai a jihohin da abin ya fi shafa.
Matsin tattalin arziki
Samu kari