Dollar zuwa Naira
NSA ya hada-kai da CBN, ‘yan sanda, kwatsam da NFIU domin a farfado da kimar Naira. Burin shi ne farashin Dalar Amurka da sauran kudin ketare su daina tashi.
Dr. Usman Bugaje ya ce kowa ya gano cewa Bola Tinubu bai da mafita game da matsalolin kasar nan. Bugaje ya ce akwai bukatar Tinubu ya nemi sabon salo.
Hukumar yaki da rashawa (EFCC) ta kai sumame ofishin wasu 'yan canjin kudi a Abuja, sun yi awon gaba da mutane 50 da ake zargin suna tsawwala farashin dala.
Atiku Abubakar ya yi magana yake cewa gwamnatin APC ta jawo karyewar Naira da matsin tattalin arziki; tshin Dala da rugujewar tattali duk laifin Bola Tinubu ne.
Kwamitin sarakunan gargajiya na Egba da ke jihar Ogun ya dakatar da wani basarake kan cin zarafin naira, an dauki matakin ne a jiya Juma'a 16 ga watan Faburairu.
Naira ta fadi zuwa N1,600 idan aka kwatanta da dala a ranar Alhamis yayin da tattalin arzikin Najeriya ke ci gaba da tabarbarewa a karkashin Shugaba Bola Tinubu.
Kamfanoni irin su BUA, Flourmills, Cadbury da ma bankuna irin su Unity na fuskantar barazana daga faduwar darajar Naira, inda suka tafka asarar naira biliyan 140.
Tsohon gwamnan jihar Bauchi, Isa Yuguda, ya ce wasu gurbatattun ‘yan siyasa ne suka haifar da faduwar darajar Naira a kasuwar duniya ta hanyar boye kudin a gidajesu.
Hukumar jin dadin Alhazai ta koka yayin da alamu suka nuna ba za ta iya cike gurbin yawan kujeru da aka ba ta ba na aikin hajji a wannan shekara.
Dollar zuwa Naira
Samu kari