Dan takara
A rahoton nan, za a samu jerin sarakuna, masu mulki, sojoji da shehunan malaman da aka rasa a shekarar 2023. Daga ciki akwai Sheikh Dr. Abubakar Giro Argungu
Mun kawo jerin ‘yan siyasan da su ka fi kowa yin asara a bana. Sun shiga takara ko aka sa ran za su samu mukami a gwamnati, amma sun tashi babu komai a 2023.
Za a ji jerin Gwamnoni da masu jiran gado da Kotu ta tsige bayan hawa mulki ko ana shirin rantsar da su a sakamakon lashe zabe da INEC ta shirya a PDP da APC.
Ahmad Yariman Bakura za su kaddamar da kungiyar da za ta goyi bayan tazarcen Bola Tinubu a 2027. Domin ganin APC ta cigaba da mulki, ‘yan siyasan sun fara shiri.
Shirin tsige Gwamnan Ribas ya yi sanadiyyar da ‘yan majalisar dokoki suka sauya sheka zuwa APC. Kuma an ji matsayar Nyesom Wike a PDP a gwamnatin APC.
Fatara tana tada tsohon bashi, ‘Yan majalisan da aka yi a 1990s sun roki gwamnatin Bola Tinubu ta biya su albashi da alawus na aikin da su ka yi a baya.
Dr. Muazu Babangida Aliyu ya ce siyasa sai mutanen banza, yake cewa tun daga wajen sayen fam zuwa zaben tsaida gwani, an yi waje da mutanen kirki daga samun mulki.
Rundunar 'yan sanda ta ce ta samu nasarar kama wani dan takarar gwamna da wasu mutane uku kan zargin satar sama da naira miliyan 607 daga manhajar Patricia.
Kafin a iya shirya zabuka masu nagarta, Attahiru Jega ya ce akwai gyare-gyaren da ake bukata, daga ciki ayi wa INEC garambawul sannan a gyara dokar zabe ta kasa.
Dan takara
Samu kari