Jihar Borno
Kamfanin rarraba wuta na kasa (TCN) ya sanar da lalacewar wutar lantarki a jihar Borno biyo bayan kai hari da wasu bata gari suka yi kan turakan wuta da ke jihar.
Gwamnatin jihar Borno ta samar da taki tirela 100 ga manona a jihar, za a sayar da takin ne kan saukin kashi 50%. Umar Usman Kadafur ne ya kaddamar da shirin.
Hukumomin kasar Saudiyya sun tabbatar da cewa wata Hajiya daga jihar Borno ta haifi jariri namiji wanda aka sanyawa suna Muhammad yayin aikin hajji.
Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya mika mulkin jihar ga mataimakinsa domin tafiya kasa mai tsarki gudanar da aikin Hajjin 2024.
Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umaru Zulum ya buɗe shirin mayar da ƴan gudun hijira zuwa gida tare da tallafa masu da kudi da kayan abinci.
Tsohon babban limamin jihar Borno, Imam Asil ya riga mu gidan gaskiya bayan fama da gajeruwar jinya da yammacin yau Juma'a 7 ga watan Yuni a birnin Maiduguri.
Kotu ta ba da belin tsohon ɗan sanda, DCP Abba Kyari bayan shafe watanni 27 a gidan gyaran hali kan zargin alaka da manyan masu hada-hadar miyagun kwayoyi.
Wasu 'yan ta'addan ISWAP sun bawa jama'ar garuruwan dake karamar hukumar Kukawa a jihar Borno zabin ko dai su bar gidajensu ko a kashe saboda zargin cin amana
'Yan ta'addan kugiyar ta'addanci ta ISWAP sun kai farmaki kan wasu masunta a jihar Borno. Miyagun ƴan ta'addan sun hallaka mutum 15 a yayin harin.
Jihar Borno
Samu kari