APC
Kotun Koli ta shirya raba gardama kan shari'ar zaben gwamnan jihar Sokoto a yau Alhamis 25 ga watan Janairu tsakanin jam'iyyun APC da kuma PDP a jihar.
Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Jos ta ki amincewa da bukatar PDP don dakatar da kakakin Majalisar jihar daga kin tabbatar da sabbin 'yan Majalisun APC 16.
Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Ganduje ya isa jihar Kano a yammacin Laraba, 24 ga watan Janairu. Zai gana da masu ruwa da tsaki a APC a ranar Alhamis.
Gwamnan jihar Ondo, Lucky Aiyedatiwa ya sallami dukkan kwamishinoni da sauran hadimai da masu rike da mukaman siyasa a jihar don inganta harkokin gwamnati.
Wani sojan baka a siyasar Kano, Dan Bilki Kwamanda, ya ce nan ba da dadewa ba za su kawo karshen siyasar jagoran NNPP, Dr. Rabiu Musa Kwankwaso..
Jam'iyyun adawa da suka hada da PDP da NNPP sun caccaki shugaban jam'iyyar APC, Abdullahi Ganduje kan kalamansa cewa matsalar zabe ba INEC ba ne illa 'yan siyasa.
Tsohon hadimin tsohon shugaban kasa, Bashir Ahmad ya bayyana cewa idan har sulhu ya tabbata tsakanin Ganduje da Kwankwaso to zata karewa PDP A 2027.
Mambobin Majalisar jihar Ogun sun tsige kakakin Majalisar, Kunle Oluomo kan badakalar makudan kudade da mulkin kama-karya, sun zabi sabon shugaba.
Jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya ta lashe zabukan dukkan kananan hukumomi 27 da kansiloli 312 a jihar Borno a zaben da aka gudanar a jiya Asabar.
APC
Samu kari