Abun Al Ajabi
Wani mai wankin mota ya tsallake rijiya da baya yayin da ya fita domin ya dana mota bayan da ya wanke ta. An bayyana irin gangancin da ya yi a yanzu.
Alhaji Abdulrahman Ado Ibrahim, Ohinoyi na kasar Ebira ya kwanta dama. Legit Hausa ta tattaro wasu abubuwa da ya kamata a sani game da basaraken mai daraja ta daya.
Wasiu Oyekan ya daki marigayi Ibrahim Lateef a wuya inda ya fadi ya buga kai a kasa, nan take ya fara fitar da jini ta hanci ta kunne inda ya ce ga garinku.
Dr Ado Ibrahim, Ohinoyi na kasar Ebira ya rasu a wani asibitin Abuja. Basaraken mai daraja ta daya ya rasu ne a ranar Lahadi, 29 ga watan Oktoba yana da shekaru 94.
A wani bidiyo da ya yadu, an gano wata amarya a tsaye tana kallon angonta da ke tikar rawa cike da murna a wajen shagalin bikinsu. Yanayin amaryar ya ta da kura.
Wata akuya ta tura kanta a cikin butan karfe sannan ta kasa fitowa daga ciki. Sai da makwabta suka taru a kanta kafin aka iya ceto ta daga cikin butan karfen.
Wasu iyali sun cika da mamaki bayan sun kama mai aikinsu da aka dauka don share harabar gida tana aika-aika. An kama ta tana haura taga don shiga ainahin gidan.
Wani mutumi da ya ce ya soya kaza ta hanyar amfani da ruwa ya yadu bayan ya saki bidiyon tsarin da ya bi. Ya dage cewa ya fi kyau a soya kaza da ruwa.
Wata dalibar aji uku a jami’ar Port Harcourt (UNIPORT), Otuene Justina Nkang, ta rasa ranta bayan saurayinta ya kashe don yin kudi a jihar Ribas.
Abun Al Ajabi
Samu kari