Abuja
Ana kyautata zaton Bola Tinubu zai yi aiki da kwararru wajen gudanar da mulkinsa. Ya zabi wasu manyan sanannun masu ilimi da gogewan da ya kamat ku sani a kai.
Lauya ya nemi a haramtawa Stella Okotete zama ɗaya daga cikin waɗanda Shugaba Tinubu zai bai wa muƙamin minista a gwamnatinsa. Lauya ya zargeta da cin hanci.
Ana sa ran a taron majaliaar koli (NEC) wanda zai gudana ranar Alhamis mai zuwa 3 ga watan Agusta, 2023, za a naɗa Ganduje a matsayin shugaban APC na ƙasa.
Rundunar 'yan sandan birnin Tarayya ta gargadi mutane kan amfani da lambobinsu wurin cin bashi a birnin da kuma amfani da layukan don cimma wata bukata ta su.
Jam'iyyar APC ta cimma matsayar cewa zata gudanar da taron shugabanni ranar 2 ga watan Agusta, 2023 yayin da taron NEC zai biyo baya ranar 3 ga watan Agusta.
Zaman ci gaba da tattauna batun rage wa ma'aikata radadin cire tallafin man fetur ya gamu da cikas yayinda aka ga wakilan ƙungiyar NlC sun fice daga ɗakin taro.
Rundunar sojin Najeriya ta yi nasarar kubutar da wadanda aka yi garkuwa da su 88 tare da hallaka 'yan ta'adda 59 bayan kwato muggan makamai daga hannun su.
Wani lauya a birnin Tarayya, Abuja, Emmanuel Ekwe ya yi barazanar maka tsohon gwamnan jihar Ebonyi, Dave Umahi a kotu idan har bai karbi mukamin minista ba.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya amince da biyan makudan kudade na alawus N25,000 ga likitoci da sauran ma'aikantan lafiya na Tarayya bayan fara yajin aiki.
Abuja
Samu kari