Majalisar dokokin tarayya
'Yan majalisar dokokin jihar Kaduna sun bayyana rashin jin dadinsu bayan tsohon gwamnan jihar, Nasir El-Rufa'i ya kira su da jahilai, marasa ilimi.
'Yan majalisar wakilai sun yi cacar baki yayin da za su fara muhawara kamn maganar dakatar da gwamna Simi Fubara da shugaban kasa Bola Tinubu ya yi.
Majalisar dokokin jihar Osun ta fara yunkurin kawo gyaran da zai dokantar da auren musulmi da ƴan addinin gargajiya, kudurin dokar ya kai karatu na 2.
Hadimin tsohon shugaban kasa, Reuben Abati ya bayyana fatan majalisar kasar nan za ta iya tsige Bola Ahmed Tinubu daga kujerarsa saboda karya dokar kasa.
Dan Majalisar Tarayya daga jihar Sokoto, Hon. Sani Yakubu ya dauki nauyin karatun wasu dalibai 21 a jami’a domin tallafa musu wajen samun ilimi mai inganci.
Shugaba Tinubu ya yi amfani da sashe na 305(1)–(6) na kundin tsarin mulki na 1999 da ya ba wa shugaban ƙasa damar ayyana dokar ta ɓaci wajen dakatar da Fubara.
Majalisar wakilai ta Najeriya ta amince da kudirin haraji da gwamnatin tarayya ta gabatar mata. Majalisar ta amince da kudirin ne bayan ya tsallake karatu na uku.
Sanata Natasha Akptoi Uduaghan ta sake nanata cewa majalisar dattawa ta dakatar da ita ne saboda ana son hana ta magana kan zargin Akpabio da cin zarafi.
Kundin tsarin mulkin Najeriya ya tanadi sashen da ya ba da damar tsige gwamna idan aka same shi da laifi. Majalisar dokoki ta jiha ce ke da alhakin tsige gwamna.
Majalisar dokokin tarayya
Samu kari