Djibouti: Dan Shekara 78 Ya Lashe Zaben Shugaban Kasa Karo na 6 a Jere a Afrika

Djibouti: Dan Shekara 78 Ya Lashe Zaben Shugaban Kasa Karo na 6 a Jere a Afrika

  • Hukumomi sun sanar da zaben shugaban kasa da aka gudanar a kasar Djibouti da ke Afrika ta Tsakiya bayan tattara kuri'un da aka kada
  • Rahotanni sun nuna cewa shugaban kasa Ismail Omar Guelleh ne ya yi nasarar lashe zaben, wanda ya zama sau shida yana nasara a jere
  • Omar Guelleh ya samu mafi rinyane kuri'u, inda ya samu sama da kashi 90, yayin da babban abokin hamayyarsa ya samu kasa da kashi 10

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Djibouti - Shugaban Djibouti mai dadadden mulki, Ismail Omar Guelleh, ya samu gagarumar nasara a zaben kasar, inda hakan ya ba shi damar fara wa’adi na shida a jere a kasar dake Afrika.

Guelleh ya samu kashi 97.81 cikin 100 na kuri’un da aka kada ranar Juma’a, a cewar sakamakon da hukumar zaben kasar ta fitar.

Kara karanta wannan

An zo wajen: An nemi a yi wa Trump gwajin kwakwalwa kan yakin Iran

Ismail Omar Guelleh yayin zabe
Shugaban Djibouti Ismail Omar Guelleh yayin kada kuri'a. Hoto: @IsmailOguelleh
Source: Twitter

Tashar Al-Jazeera ta sanar da cewa abokin takararsa, Mohamed Farah Samatar, ya samu kashi 2.19 cikin 100 na kuri’un.

Ismail Guelleh ya ci zaben Djibouti

Jim kadan bayan tattara sakamakon zabe da sanarwar hukuma, shugaba Ismail Omar Guelleh ya fito ya yi magana kan nasarar da ya samu.

“An sake zabena,”

In ji Guelleh mai shekaru 78

“Da ikon Allah muka kai nan, muna fatan hakan zai kare da nasara,”

In ji Guelleh ga manema labarai yayin da yake kada kuri’arsa a zauren majalisar birnin Djibouti da tsakar rana a ranar Juma’a.

A bara ne kasar ta cire iyakar shekarun takarar shugaban kasa, abin da ya ba shi damar neman karin wa’adi na shekaru biyar a bana.

Rahotanni sun nuna cewa yawan masu kada kuri’a ya kai kashi 80.4 cikin 100 a ranar Juma’a. Kimanin kashi 1 bisa 4 na al’ummar kasar, wato kusan mutane 256,000.

Kara karanta wannan

Tsadar man fetur: Tinubu ya nuna kukan dadi 'yan Najeriya ke yi

Lokacin da Guelleh ya fara mulki

Rahotanni sun tabbatar da cewa shugaba Guelleh yana mulkin kasar Djibouti mai yawan jama’a kusan miliyan 1 tun shekarar 1999.

Kasashen makwabta kamar Eritrea, Ethiopia da Somalia suna kewaye da kasar, wacce ke da muhimmancin matsayi a mashigar Bab al-Mandeb da ke ba da damar shiga Tekun Bahar Maliya daga Tekun Aden.

Yadda aka yi kamfen a Djibouti

Duk da cewa mutane sun fita kada kuri’a a ranar Juma’ar data gabata, kadan ne suka yi shakka a kan wanda zai yi nasara a zaben, inda hasashe ya karkata kan Guelleh.

An ce dubban mutane sun halarci gangamin yakin neman zaben Guelleh kafin zaben, yayin da hotunansa suka mamaye babban birnin kasar.

Ismail Omar Guelleh
Ismail Omar Guelleh na hira da 'yan jarida bayan kada kuri'a. Hoto: @IsmailOguelleh
Source: Twitter

Ana tsadar fetur a Afrika

A wani labarin, kun ji cewa Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya nuna cewa kasashen Afrika da dama na fama da matsalar tsadar fetur.

Shugaba Bola Tinubu ya buga misali da kasar Kenya da ya ce ta fi Najeriya tsadar man fetur da ya biyo bayan yakin Iran da Amurka.

Tinubu ya yi magana ne a jihar Bayelsa yayin bude wasu muhimman ayyuka a daidai lokacin da 'yan Najeriya ke korafi kan tashin farashi.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng