APC Ta Fadi Abin da Zai Hana 'Yan Adawa Kwace Mulkin Najeriya

APC Ta Fadi Abin da Zai Hana 'Yan Adawa Kwace Mulkin Najeriya

  • Shugaban APC na kasa, Farfesa Yilwatda Nentawe ya soki jam’iyyun adawa kan rikice-rikicen cikin gida da kokarin da suke na neman muklin Najeriya
  • Ya ce rashin daidaito alama ce ta rashin shiri na shugabanci, saboda haka tana kasa tana dabo a kan yunkurinsu na neman korar Bola Tinubu daga ofis
  • Farfesa Nentawe ya gargadi ‘yan Najeriya su yi taka-tsantsan wajen zaben shugabanni, domin kada su yi zaben tumun dare a babban zabe mai zuwa

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar – Shugaban APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya bayyana cewa rikice-rikicen cikin gida da ke addabar yawancin jam’iyyun adawa alama ce karara da ke nuna ba su shirya rike ragamar shugabancin kasa ba.

Farfesa Yilwatda ya bayyana hakan ne a Abuja yayin da yake jawabi kan muhimman batutuwan da suka shafi tafiyar da harkokin zamantakewa, siyasa da tattalin arzikin kasa.

Kara karanta wannan

Bayan barazanar APC, an kafa kwamiti game da sauya shekar gwamnan Bauchi

APC ta yi wa yan adawa shagube
Nentawe Yilwatda yana jawabi ga yan jarida Hoto: Prof Nentawe Yilwatda
Source: Twitter

Daily Trust ta wallafa cewa Yilwatda ya ce duk wata jam’iyya da ta kasa tafiyar da al’amuranta na cikin gida yadda ya kamata, ta kasa sasanta sabanin ra’ayi tsakanin 'ya'yanta, ba za ta iya da Najeriya ba.

Jam'iyyar APC ta soki yan adawa

The Cable ta wallafa cewa Shugaban APC ya ce, rashin iya tafiyar da gida shi ne babban dalilin da ke nuna cewa irin wadannan jam’iyyu ba su da kwarewar da ake bukata domin tafiyar da al’amuran kasa yadda ya kamata.

A cikin wata sanarwa da mai ba shi shawara kan harkokin yada labarai, Mista Abimbola Tooki, ya fitar, shugaban ya ce rikice-rikicen da ke yawan faruwa a cikin jam’iyyun adawa alamu ne na gazawa.

Ya bayyana wasu daga cikin rigingimun sun hada da rabuwar kai, shari’o’i, takaddama tsakanin bangarori, da kuma abin da ya kira rashin akida mai karfi.

Shawarar APC ga 'yan Najeriya

Kara karanta wannan

Akwai kura: Shugaban INEC ya hango babbar barazana kan zaben 2027

Nentawe Yilwatda ya kara da cewa zai zama babban hadari idan ‘yan Najeriya suka mika makomar kasar nan ga ‘yan siyasar da suka gaza tabbatar da tsari da doka a cikin jam’iyyunsu.

Nentawe Yilwatda ya ja kunnen masu zabe
Shugaban APC na kasa tare da wasu daga cikin yan Najeriya Hoto; Prof Nentawe Yilwatda
Source: Twitter

Ya ce:

“Jam’iyyar da ba ta iya tafiyar da kanta ba, ba za ta iya tafiyar da Najeriya ba. Idan wata jam’iyya na yawan fada cikin rikice-rikice da kanta ke haddasawa, tana fama da cin amanar cikin gida, kuma rashin kyakkyawan shugabanci ke raunana ta, to bai kamata ta nemi amanar ‘yan Najeriya ta jagoranci kasa ba.”

Shugaban APC ya bukaci ‘yan Najeriya su kasance masu hikima wajen bambance gaskiya da hayaniya, shiri na gaskiya da farfaganda, da kuma bambancin son kai da nagartaccen shugabanci.

Nafiu ya karyata zancen yi wa APC aiki

A baya, mun wallafa cewa Shugaban tsagin ADC na kasa Nafi’u Bala, ya zargi sababbin shigowa jam'iyyarsu da haddasa rikice-rikice a cikin jam'iyyun da suka bari, kuma da neman kwace masu ta su.

Ya bayyana cewa tsofaffin ‘yan jam’iyya sun dade suna tafiyar da ADC cikin lumana kafin zuwan mutanen da aka ba su mafaka, kuma suke kokarin rikita masu tafiya tare da neman kwace jam'iyyar.

Nafi'u Bala ya yi magana game da zargin cewa ya karbo wata kwangila ne domin ya hana 'yan adawa katabus gabanin zaben 2027 inda ya yi mamakin dalilin da zai sa shi ya cefanar da jam'iyyarsa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng