"Ba Kwankwaso ba"; An Sanar da Gwamna Abba Wanda Zai Sa Ya Lashe Kano a 2027
- Wani na kusa da tsohon shugaban jam'iyyar APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya yi magana kan siyasar jihar Kano
- Malam Umar Idris Shuaibu ya kwantar da hankalin Gwamna Abba Kabir Yusuf kan batun tazarce a zaben shekarar 2027
- Ya bayyana cewa Abdullahi Umar Ganduje na aiki tukuru domin ganin ya sake komawa kan kujerarsa a karo na biyu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Kano - Wani na kusa da tsohon shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje, mai suna Malam Umar Idris Shuaibu, ya aika sako ga Gwamna Abba Kabir Yusuf.
Malam Umar Idris Shuaibu ya sanar da Gwamna Abba ya kwantar da hankalinsa, inda ya ba shi tabbacin cewa Ganduje yana nan yana aiki domin tabbatar da nasararsa a jihar a shekarar 2027.

Source: Facebook
Malam Umar Idris Shuaibu ya bayyana hakan ne a ranar Litinin, 6 ga watan Afrilun 2026 yayin wata hira ta musamman da jaridar The Punch.
Wane tabbaci aka ba Gwamna Abba?
A lokacin tattaunawar ya yi tsokaci mai faɗi kan yadda yanayin siyasar jihar Kano ke sauyawa da kuma rawar da Ganduje ke takawa wajen fito da tasirin jam’iyyar gabanin babban zaɓe mai zuwa.
Ya kwatanta Ganduje a matsayin "janar na siyasa" wanda tasirinsa a siyasar Kano ba shi da tamka, yana mai cewa iyawarsa ta gina maslaha da tafiyar da buƙatun siyasa ita ce ta ci gaba da bayyana ƙarfin APC a jihar.
A cewarsa, Ganduje ya taka rawar gani wajen daidaita jam’iyyar ta hanyar lallashin dukkan masu neman takarar gwamna a ƙarƙashin APC da su janye su marawa Gwamna Abba baya domin tabbatar da haɗin kai da dorewar jam’iyyar.
“Ana buƙatar shugaba mai zurfin hikimar siyasa da tasiri wajen gamsar da masu takara masu ƙarfi su janye domin manufa guda. Ganduje ya yi hakan cikin nasara, kuma hakan ya nuna ƙarfinsa a matsayin mai haɗa kan mutane kuma masani kan dabarun yaƙi."

Kara karanta wannan
Abba da Ganduje sun yi zaman sirri kan batun mataimaki, sarki da wasu matsaloli a Kano
"Ka kwantar da hankalinka, Ganduje yana nan yana aiki tuƙuru kuma zai ba ka Kano. Kwarewarsa ta siyasa da ƙarfin shugabancinsa ba su da tamka.”
- Malam Umar Idris Shuaibu
Ganduje ya samu yabo a siyasar Kano
Ya nanata cewa zurfin fahimtar da Ganduje yake da ita kan yanayin siyasar Kano, tare da yadda mutanen karkara ke son sa, sun sanya shi zama babban jigo wajen yanke hukunci kan sakamakon zaɓukan da za a yi a nan gaba a jihar.
“Ƙarfinsa yana ga yadda yake da alaƙa da mutanen karkara da kuma iyawarsa ta tara goyon baya cikin sauri. Wannan ne ya sa masu ruwa da tsaki da dama har yanzu suke dogara da shugabancinsa."
- Malam Umar Idris Shuaibu

Source: Facebook
An ba 'yan siyasar Kano shawara
Malam Umar Idris Shuaibu ya yi kira ga ’yan siyasa a jihar da su ba da fifiko ga haɗin kai da zaman lafiya, inda ya jaddada cewa haɗin kai a cikin jam’iyya shi ne jigon samun nasara a zaɓe.
Ya nuna kyakkyawan fata cewa tare da ci gaba da jagorancin Ganduje da dabarunsa, APC za ta ci gaba da kasancewa mai ƙarfi kuma tana da damar samun nasara a Kano da ma wasu wuraren a shekarar 2027.

Kara karanta wannan
An buga kugen siyasa; Kwankwaso ya sa labule da Atiku, an ji abin da suka tattauna
Gwamna Abba ya fara zawarcin Shekarau
A wani labarin kuma, kun ji cewa Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya gana da Sanata Ibrahim Shekarau.
Gwamna Abba ya gana da Shekarau ne domin duba yiwuwar jawo shi zuwa jam'iyyar APC yayin da ake ci gaba da shirye-shiryen zaben 2027.
Majiyoyi sun bayyana cewa Gwamna Abba na ƙoƙarin shimfiɗa dabaru tun da wuri domin tabbatar da cewa ya ci gaba da riƙe kujerarsa bayan zaɓen 2027.
Asali: Legit.ng
