An Gano Jam’iyyu 2 da Atiku, Kwankwaso Za Su Iya Komawa saboda Tsaro Kafin 2027

An Gano Jam’iyyu 2 da Atiku, Kwankwaso Za Su Iya Komawa saboda Tsaro Kafin 2027

  • Wasu rahotanni sun nuna cewa Atiku Abubakar, Peter Obi da Rabiu Musa Kwankwaso na shirin barin ADC gabanin zaben 2027
  • Rikicin shugabanci da matakin INEC ya jefa ADC cikin rudani mai tsanani wanda ake fargabar zai iya jawo mata asara a zaben
  • Majiyoyi sun ce yan siyasar na duba yiwuwar komawa jam’iyyu 2 a matsayin mafita domin gudun ka da lokaci ya kure masu

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Rahotanni sun nuna cewa manyan ‘yan adawa a Najeriya na duba yiwuwar barin jam’iyyar ADC gabanin babban zaben 2027.

Cikin manyan jagororin da ke tattaunawa akwai Atiku Abubakar, Peter Obi da kuma Rabiu Musa Kwankwaso.

An ce Atiku, Kwankwaso da Obi sun fara tunanin barin ADC
Sanata Rabiu Kwankwaso, Atiku Abubakar da Peter Obi. Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso, Atiku Abubakar da Peter Obi.
Source: Twitter

Musabbabin neman mafita ga Atiku, Kwankwaso daga ADC

An ce wannan mataki na da nasaba da rikicin shugabanci da ya dabaibaye jam’iyyar ADC, wanda ya janyo rikice-rikicen cikin gida, cewar rahoton The Guardian.

Kara karanta wannan

Matakin INEC game da shugabannin ADC ya tafi gaban Trump da majalisar Amurka

Hakan ya kara tsananta ne bayan da INEC ta dakatar da amincewa da dukkan bangarorin shugabancin jam’iyyar.

Matakin ya biyo bayan hukuncin kotun daukaka kara da kuma karar da ake yi kan tsarin shugabancin jam’iyyar.

Masana harkokin siyasa sun yi gargadin cewa wannan rikici na iya hana ADC damar tsayar da ‘yan takara a zaben 2027.

Sun ce idan aka ci gaba da wannan hali, jam’iyyar na iya fuskantar matsaloli wajen shiga zaben shugaban kasa, gwamnoni da ‘yan majalisa.

Majiyoyi sun bayyana cewa shari’o’in da ke gudana na iya shafar duk wani dan takara da zai tsaya karkashin jam’iyyar ADC.

Majiyar ta ce:

“Idan wannan rikici ya ci gaba, kuma mambobi suka tsaya takara karkashin ADC, sannan daga baya aka soke amincewa da jam’iyyar, ba za su iya kawai sauya sheka zuwa wata jam’iyya ba.”
INEC ta yi fatali da shugabancin ADC
Shugaban Hukumar INEC a Najeriya, Joash Amupitan. Hoto: INEC Nigeria.
Source: Facebook

Jam'iyyun da ake sa ran za su koma

Hakan ya sa shugabannin ‘yan adawa suka fara tattaunawa a boye domin nemo mafita kafin lokaci ya kure musu.

Ana sa ran za su gudanar da wasu muhimman tarurruka a Abuja bayan hutun 'Easter' domin yanke hukunci kan makomar siyasa.

Kara karanta wannan

Rikicin ADC: Jam'iyyar adawa ta roki Kwankwaso, Atiku da Obi su dawo cikinta

Rahotanni sun ce suna duba yiwuwar amfani da jam’iyyun APP da kuma NDC a matsayin mafita.

Masana sun ce matakin da za su dauka na iya sauya yanayin siyasar Najeriya gabanin zaben 2027 wanda ake ganin zai yi matukar zafi sosai.

Sanata Rabiu Kwankwaso shi ne na karshe da ya dawo ADC a cikin jiga-jigan siyasar Najeriya bayan murabus daga jam'iyyar NNPP da ya yi takara a zaben 2023.

Jam'iyyar adawa na zawarcin Atiku, Kwankwaso

A baya, an ji cewa wata jam’iyyar adawa a Najeriya ta bukaci manyan ‘yan adawa kamar Atiku Abubakar, Peter Obi da Rabiu Kwankwaso su dawo cikinta.

Jam'iyyar ta bayyana haka ne domin ceto dimokuradiyya a Najeriya wanda ake zargin ana neman rikita jam'iyyun hamayya.

Hakan na zuwa ne yayin da jam'iyyar ADC ta sake burmawa cikin matsala wanda ake zargin gwamnatin APC da hannu a cikin rikicin da take fama da shi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.