APC Ta Karbe Ikon Majalisa Gaba Daya da Mamban PDP Tilo Ya Koma Jam’iyyar
- Jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya ta kwace cikakken iko a majalisar Gombe bayan dan PDP na karshe ya sauya sheka
- Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya ya ce matakin na nuna amincewar jama’a da gwamnatinsa da kuma APC
- 'Dan majalisar ya ce salon shugabanci ne ya ja hankalinsa zuwa APC inda ya sha alwashin ba ta dukkan goyon baya
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Akko, Gombe - Gwamnan Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya kara karfafa rinjayen jam’iyyar APC a jihar bayan sauya shekar dan majalisar PDP.
Majiyoyi sun tabatar da cewa wannan sauya sheka ta mamban ta tabbatar wa APC cikakken iko a majalisar kasancewa shi ne na karshe daga jam’iyyar PDP.

Source: Facebook
Hakan na cikin wata sanarwa da daraktan harkokin yada labarai na gidan gwamnati, Ismaila Uba Misilli ya fitar a shafinsa na Facebook.
'Dan majalisar PDP tilo ya koma APC
'Dan majalisar, Yakubu Daniel, wanda ke wakiltar mazabar Billiri Gabas, ya sanar da ficewarsa daga PDP zuwa APC, lamarin da ya bar majalisar ba tare da ‘yan adawa ba.
Misilli ya bayyana cewa sauya shekar wani bangare ne na ci gaba da sauyin da ake gani a jihar musamman abubuwan ci gaba da Gwamna Inuwa ke kawowa.
Sanarwar ta nuna cewa wasu ‘yan majalisar adawa, ciki har da shugabannin marasa rinjaye, sun riga sun sauya sheka zuwa APC tun kafin wannan mataki.

Source: Twitter
Martanin Gwamna Inuwa kan karuwar APC
Yayin karbar dan majalisar a Gombe, gwamna Inuwa Yahaya ya bayyana cewa wannan lamari wata alama ce ta amincewar jama’a da salon mulkinsa da kuma yadda APC ke tafiyar da gwamnati.
Ya kuma tabbatar masa da adalci da hada kai da kuma ba kowa dama a cikin jam’iyyar, yana mai cewa APC na kokarin tabbatar da cigaba mai dorewa.
Gwamnan ya kara da cewa karuwar rinjayen jam’iyyar a dukkan mazabu na nuna yadda jama’a ke kara yarda da manufofi da shirye-shiryen gwamnatinsa.
Haka kuma ya danganta hakan da manufar “Renewed Hope” ta Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu wanda ke ci gaba da inganta rayuwar 'yan Najeriya baki daya.
A nasa bangaren, Yakubu Daniel ya ce ya yanke shawarar komawa APC ne saboda yadda gwamna ke tafiyar da mulki cikin gaskiya da rikon amana.
Ya yi alkawarin biyayya ga jam’iyyar tare da kokarin bayar da gudunmawa domin cigaban APC a mazabarsa da ma daukacin jihar Gombe.
An zabi Igbo cikin shugabannin APC a Arewa
Tun farko, kun ji cewa wani ɗan asalin Anambra ya zama mataimakin sakataren jam'iyyar APC a Gombe ta hanyar yarjejeniya da aka yi.
Edwin Chukwujekwu ya ce nasararsa ta nuna haɗin kai da adalcin APC, inda ya jaddada cewa ba a ware kowa a cikin jam’iyyar ba domin tabbatar da adalci a tsakani.
Shugaban kwamitin zaɓe, Danjuma Dabo, ya ce zaɓen yarjejeniya na cikin kundin tsarin APC, yana ƙarfafa haɗin kai domin zaben shekarar 2027 da ake tunkara.
Asali: Legit.ng

