2027: An Rugurguza Allunan Tallata Tinubu, 'Yan APC na Korafi
- Wasu matasa a jihar Ondo sun yi Allah-wadai da lalata allunan kamfen din Bola Tinubu, suna zargin ‘yan siyasa da hannu a barnar da aka yi
- Ƙungiyar matasan ta ce tana da hujjoji kan waɗanda suka aikata laifin, amma akwai matakan da za ta dauka kafin gurfanar da su a kotu
- Rahotanni sun ce matasan sun yi gargadin cewa ba za su lamunci irin haka ba, kuma sun yi kira ga hukumomi su kare kayan kamfen
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Ondo - Wata ƙungiyar matasa ta siyasa a jihar Ondo mai suna Akure Youth for BTO, wadda ke goyon bayan sake zaɓen Bola Tinubu, ta yi Allah-wadai da lalata allunan kamfen ɗinta.
A korafin da kungiyar ta yi, ta bayyana cewa wasu da ake zargin ‘yan siyasa ne suka ɗauki nauyin a lalata allunan da ke dauke da hoton shugaban kasa Bola Tinubu.

Source: Twitter
Tribune ta rahoto cewa kungiyar ta bayyana lamarin a matsayin laifi da wasu ‘yan daba na siyasa suka yi domin dakile halastattun ayyukanta na siyasa, tana mai cewa hakan bai dace ba.
An gano masu rusa allunan Bola Tinubu
A cikin wata sanarwa da sashen yaɗa labarai na ƙungiyar ya fitar, ta ce hotunan na’urar sa ido ta gano waɗanda ke da hannu a lamarin, tare da ƙarawa da cewa suna da hujjoji a hannunsu.
Sai dai ƙungiyar ta ce duk da hujjojin, ba za ta ɗauki matakin shari’a nan take ba domin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali, amma ta yi alƙawarin maye gurbin allunan da aka lalata domin ci gaba da kamfen ɗinta.
Ta kuma yi gargadin cewa cigaba da lalata wuraren zai jawo daukar matakin doka, ciki har da mika hujjoji ga hukumomin tsaro da kuma jama’a.
Sanarwar ta ce:
“Wannan lamari cin zarafin ginshiƙan dimokuraɗiyya ne da yaki da ‘yancin faɗar albarkacin baki."
“Lalata kayan kamfen da aka kafa bisa doka da wasu ‘yan siyasa suka yi laifi ne da ke raunana tsarin dimokuraɗiyya da kuma barazana ga gudanar da siyasa cikin lumana.
Kiran matasan ga jami'an tsaro
Punch ta rahoto cewa kungiyar ta kuma buƙaci hukumomin tsaro su ƙara sa ido tare da tabbatar da kare kayan kamfen da kuma haƙƙin ‘yan ƙasa na shiga harkokin siyasa cikin ‘yanci.
Ta sake jaddada aniyarta na gudanar da kamfen cikin lumana da kuma mai da hankali kan muhimman batutuwa, tare da bayyana goyon bayanta ga sake zaɓen shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Source: Facebook
An so kashe malami dan siyasa
A wani labarin, mun kawo muku cewa malamin addinin Musulunci da ya ayyana cewa zai nemi takarar gwamna a Sokoto ya ce an turo a kashe shi.
Legit Hausa ta rahoto cewa Sheikh Bashir Sani Ahmad Sokoto ya sanar da cewa an kama wani mutum da ya je gidan shi domin kashe shi.
Mutumin da aka kama ya nuna cewa daga Yabo aka turo shi, kuma bayan masa tambayoyi an mika shi ga rundunar 'yan sandan jihar Sokoto.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

