Yanzu ta tabbata, Kwankwaso Zai Fice daga NNPP, An Faɗi Jam'iyyar da Zai Koma

Yanzu ta tabbata, Kwankwaso Zai Fice daga NNPP, An Faɗi Jam'iyyar da Zai Koma

  • Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya kammala shirye-shiryen komawa jam'iyyar ADC domin fuskantar zaben shekarar 2027
  • Kakakin kungiyar Kwankwasiyya ya bayyana cewa jagoran nasu fice daga jam'iyyar NNPP a hukumance a gidansa na Miller Road
  • An ba dukkan mambobin Kwankwasiyya umarnin gaggawa na su garzaya mazabunsu domin yin rajista da jam'iyyar ADC

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Jagoran darikar Kwankwasiyya na ƙasa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya ba mambobinsa umarnin sauya sheka zuwa jam'iyyar ADC.

Wannan sanarwa tana zuwa ne a matsayin wani babban matakin siyasa da tsohon gwamnan na jihar Kano ya ɗauka domin fuskantar zaɓen shekarar 2027.

Sanata Rabiu Musa Kwankwaso zai sauya sheka daga NNPP zuwa APC a ranar Litinin.
Sanata Rabiu Musa Kwankwaso yana jawabi ga manema labarai. Hoto: @KwankwasoRM
Source: Facebook

Kwankwaso zai sauya sheka zuwa ADC

Wannan na kunshe ne a cikin sanarwar da mai magana da yawun Kwankwaso, Hon. Saifullahi Hassan ya wallafa a shafinsa na X.

Kara karanta wannan

Ja'oji: Ana tsakiyar taron APC, 1 daga cikin manyan hadiman Tinubu ya yi murabus

A cikin sanarwar, an ruwaito kakakin ƙungiyar Kwankwasiyya, Dr. Habibu Sale Mohammed, ya ce Kwankwaso ya kammala dukkan tsare-tsare na shiga jam'iyyar hadakar 'yan adawa.

Ƙungiyar Kwankwasiyya ta sanar da mambobinta da sauran jama'a cewa jagoransu zai yi rajista da sabuwar jam'iyyar tasa a hukumance ranar Litinin mai zuwa.

Za a gudanar da wannan taro ne da misalin ƙarfe 12:00 na rana a gidan Kwankwasiyya dake Miller Road a cikin birnin Kano.

An tsara cewa Sanata Kwankwaso zai karɓi katin jam'iyyar ADC a gaban dubun-dubatar magoya bayansa waɗanda ake sa ran za su cika gidan nasa.

Umarni ga 'ya'yan Kwankwasiyya a Najeriya

Biyo bayan wannan mataki, an umarci dukkan 'yan ƙungiyar Kwankwasiyya dake fadin Najeriya da su garzaya su yi rajista da jam'iyyar ADC a mazaɓunsu, in ji rahoton Daily Trust.

Dr. Habibu ya jaddada cewa ya zama dole mambobi su shiga harkokin jam'iyyar a matakin gundumomi da ƙananan hukumomi domin tabbatar da nasarar sabuwar tafiyar.

An buƙaci magoya bayan da su jajirce wajen ganin jam'iyyar ta samu gindin zama a kowane lungu da sako na ƙasar nan gabanin 2027.

Kara karanta wannan

Ta faru ta kare: Mataimakin gwamnan Kano, Gwarzo, ya yi murabus daga mukaminsa

Dalilin sauya sheƙar Kwankwaso zuwa ADC

Kakakin Kwankwasiyya ya bayyana cewa wannan mataki an ɗauke shi ne domin kare muradun dimoƙuradiyya da kuma samar da kyakkyawan shugabanci a faɗin Najeriya.

Sanarwar ta ƙara da cewa Kwankwasiyya tana son gina ƙasa da za ta jibinci lamuran kowa da kowa inda za a girmama ra'ayin talakawa a duk lokacin zaɓe.

Wannan sauya sheƙa na Kwankwaso na nuna cewa jam'iyyar NNPP ta rasa babban bango majinginarta, kuma ba lallai ne ta yi tasiri a zaben 2027 ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com