APC Ta Yi Babban Rashi, Manyan Wakilan Jam'iyyar 3 Sun Mutu a Hatsarin Mota

APC Ta Yi Babban Rashi, Manyan Wakilan Jam'iyyar 3 Sun Mutu a Hatsarin Mota

  • Yayin da ake gudanar da babban taron jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya, wasu daga cikin mambobinta sun mutu a Nasarawa
  • Wasu daga cikin wakilan jam’iyyar APC uku daga Ogbadibo a Benue sun rasu bayan hatsarin mota yayin tafiya zuwa taron shiyyar Arewa ta Tsakiya
  • Rahotanni sun nuna cewa motar da ke dauke da su ta kwace ta fada cikin daji, inda kusan mutane 10 suka jikkata kuma ake kula da su a asibiti

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Makurdi, Benue - Akalla wakilan jam’iyyar APC uku daga karamar hukumar Ogbadibo a Benue sun rasu a hatsarin mota da ya rutsa da su a Nasarawa.

Lamarin ya faru ne yayin da suke tafiya Lafia ta jihar Nasarawa inda wasu 10 suka jikkata sakamakon hatsarin mota mai muni da ya afku.

Kara karanta wannan

Lamari ya girma: An maka Trump a kotu bayan bankada a takardun Eipstein

Wakilan APC sun mutu a hatsarin mota
Taswirar jihar Benue da wakilan APC da suka mutu suka fito. Hoto: Legit.
Source: Original

Hatsarin mota ya rutsa da yan APC

Leadership ta ruwaito cewa wadanda abin ya shafa suna kan hanyarsu daga Makurdi zuwa Lafia domin halartar taron shiyyar Arewa ta Tsakiya na jam’iyyar lokacin da hatsarin ya faru.

Wani babban jami’in APC ya bayyana cewa motar bas da ke dauke da wakilan ta kwace, ta fada cikin daji, inda uku suka mutu, sauran kuma suka samu raunuka.

Ya kara da cewa wadanda suka jikkata na karbar magani a asibitin koyarwa na Jami’ar Benue, yayin da ake sa ran wasu za a sallame su bayan samun sauki.

Gwamna ya kadu bayan mutuwar wakilan APC a Benue
Gwamna Alia Hyacinth na jihar Benue a gidan gwamnati da ke Makurdi. Hoto: Ali Hyacinth.
Source: Facebook

Abin da Gwamna Alia ya yi

Gwamnan Benue, Hyacinth Alia, ya ziyarci wadanda suka jikkata a asibiti bayan kammala taron jam’iyyar, domin duba halin da suke ciki da kuma jajanta musu.

An kwantar da wadanda suka ji rauni ne yayin hatsarin mota a asibitin koyarwa na Jam'iar jihar Benue da ke birnin Makudir a jihar.

Kara karanta wannan

Bayan Amurka, Trump zai tafi Venezuela neman takarar shugaban kasa

Mataimakin gwamna, Sam Ode, ya bayyana lamarin a matsayin mai tayar da hankali, yana cewa ya jawo bakin ciki ga iyalai, jam’iyya da daukacin al’umma.

Ya kuma jajanta wa iyalan wadanda suka rasu tare da fatan samun sauki ga wadanda suka jikkata, yana mai tabbatar da goyon bayan gwamnati a gare su.

Hukumar kiyaye hadurra ta kasa FRSC ta bayyana cewa hatsarin ya faru ne a Nasarawa, inda suka dauki matakan gaggawa, kodayake cikakken bayani bai kammala ba, cewar Daily Post.

Jam'iyyar APC dai ta gudanar da tarukanta da aka yi a yankunan Najeriya baki daya yayin da ake tunkarar zaben shekarar 2027 wanda ake ganin za a kai ruwa rana.

Shugaba APC, yan siyasa sun mutu a Kogi

Idan za ku iya tunawa, a baya mun baku labarin cewa jam’iyyar APC a jihar Kogi ta girgiza sakamakon rasuwar mambobinta uku da suka hada da masu ba wa gwamna shawara da shugaban mazaba.

Gwamna Ahmed Usman Ododo ya mika sakon ta'aziyya ga iyalai da abokan arzikin mamatan tare da yaba wa irin gudunmawar da suka bayar.

Hon. Onojah James Ignatius ya rasu ne a ranar Asabar 10 ga watan Maris din shekarar 2026 a birnin Lokoja bayan ya dawo daga ziyarar da ya kai wa mahaifarsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.