Tuna Baya: Yadda Sanata Shehu Sani Ya Kwarewa Jam'iyyar APC Baya

Tuna Baya: Yadda Sanata Shehu Sani Ya Kwarewa Jam'iyyar APC Baya

  • Tsohon sanatan Kaduna ta Tsakiya, Sanata Shehu Sani, ya nuna damuwa kan yadda masu rike da madafun iko ke yaudarar jama'a a lokacin zaben
  • Sanata Shehu Sani ya koka kan yadda mutanen da suka sace dukiya suke raba kayayyaki irinsu taliya domin samun kuri'u a lokacin zabe
  • Ya nuna cewa ana barin mutane cikin wahala bayan an sace musu dukiya sannan a dawo ana binsu da taliya domin su sayar da 'yancinsu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - An fitar da wani tsohon bidiyo na Sanata Shehu Sani yana yin muhimmin kira ga 'yan Najeriya kan sayar da kuri'a.

Tsohon sanatan na Kaduna ta Tsakiya ya nuna damuwa kan yadda ake ba mutane 'yan kananan abubuwa domin janye ra'ayinsu su sadaukar da kuri'unsu.

Shehu Sani ya yi magana kan sayar da kuri'a
Tsohon sanata mai wakiltar Kaduna ta Tsakiya, Sanata Shehu Sani @ShehuSani
Source: Twitter

Shafin @ADCVanguard na manhajar X ne ya sanya tsohon bidiyon a ranar Alhamis, 26 ga watan Maris na shekarar 2026.

Kara karanta wannan

Yaki da Iran: Sabani ya shiga tsakanin Trump da Netanyahu, sun yi musayar yawu

An fitar da tsohon bidiyon Shehu Sani

A cikin bidiyon tsohon sanatan ya kwancewa 'yan siyasa zani a kasuwa kan yadda suke yaudarar jama'a don su samu kuri'u.

Duk da dai bai ambaci suna ba, alamu na nuna cewa kalamansa ya yi su ne kan jam'iyyar APC a lokacin zaben shekarar 2023.

Tsohon sanatan dai ya kasance a bangaren adawa a lokacin zaben shekarar 2023 bayan ya fice daga jam'iyyar APC mai mulki.

Shehu Sani ya soki halin 'yan siyasa

A cikin bidiyon Shehu Sani ya nuna cewa 'yan siyasa na barin jama'a cikin wahala yayin da suke wawushe dukiyar kasa, sannan idan lokacin zabe ya zo su yi ta raba taliya don samun kuri'u.

Ya bayyana cewa bayan sun sace kudaden sun bar jama'a cikin wahala, sai su zo suna raba musu 'yan kananan abubuwa domin su samu kuri'unsu ta yadda za su sake komawa kan madafun iko.

Tsohon sanatan ya koka da cewa abubuwan da ake rabawa wadanda suka hada har da taliya, ba su tsinanawa jama'a komai.

Kara karanta wannan

2027: Atiku ya samu goyon baya a ADC, an nuna shi a matsayin dan takara

Shehu Sani ya koka kan sayar da kuri'u
Sanata Shehu Sani wanda ya taba wakiltar Kaduna ta Tsakiya Hoto: @ShehuSani
Source: Twitter

Me Shehu Sani ya ce kan 'yan siyasa?

"Sun sace kudi su da iyalansu ku kuma biyan kudin makaranta, biyan kudin asibiti, biyan kudin haya ya gagare ku, mutanen nan sun boye kudi sun sace muku kudi, wai sai yanzu da lokaci ya yi za ku canja su, sannan su dauki irin wannan taliya."
"Taliyar da idan ka ci yau zuwa anjima cikinka ba komai, a ce shi za su yi amfani da shi don ku sake ba su kuri'u, shin ko za ka sayar da kanka, ko za ki sayar da kanki ai sai ku amshi abu mai gwabi"

- Sanata Shehu Sani

Shehu Sani ya magantu kan 'yan bindiga

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon sanatan Kaduna ta Tsakiya, Sanata Shehu Sani ya yi magana kan matsalar 'yan bindiga da 'yan ta'adda da ake fama da ita a Najeriya.

Sanata Shehu Sani ya ce dole ne ’yan Najeriya su tashi tsaye su yi turjiya ga ’yan ta’adda, ’yan bindiga da sauran masu aikata laifufffuka da ke addabar kasar nan.

Tsohon sanatan na Kaduna ta Tsakiya ya jaddada cewa babu wata kasa daga waje da za ta zo ta ceto 'yan Najeriya da su daga wannan kalubale.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng