'Malamin Musulunci' Ya Kunyata Peter Obi, Ya Yi Karin Haske da aka Ce DSS Sun Cafke Shi
- Malamin addinin Musulunci daga Kaduna, Sheikh Ahmad Umar, ya yi magana kan ikirarin cewa jami'an tsaro.
- Sheikh Ahmad ya musanta ikirarin kama shi da DSS bayan ziyarar Peter Obi, yana karyaya labarin da cewa an yi don yaudarar mutane
- Peter Obi ya ce an kama malamin bayan ya karɓe shi a Kaduna, yana gargadin koma baya ga dimokuradiyya da barazana ga ’yancin faɗar albarkacin baki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kaduna - Sheikh Ahmad Umar, malamin Musulunci da ke Kaduna, ya karyata rahotannin da ke cewa DSS ta kama shi.
Hakan ya biyo bayan ziyarar Peter Obi a jihar wanda tsohon gwamnan ya ce an cafke malamin bayan ganawarsu.

Source: Twitter
Peter Obi ya yi ikirarin cafke malamin Kaduna
A wani sako da ya wallafa a shafinsa na X ranar Talata 24 ga watan Maris din shekarar 2026, Obi ya yi zargin cewa an kama Umar jim kadan bayan ya karɓe shi a Kaduna.
Dan jam’iyyar ADC ya bayyana lamarin a matsayin alamar tabarbarewar dimokuradiyya, yana gargadin karuwar barazana ga ’yancin magana da bayyana ra’ayi a siyasa.
Ya ce:
“An sanar da ni cewa an kama babban malamin addini Sheikh Ahmad Tijjani Umar bayan ya mun gana."
Malamin ya musanta rahoton cafke shi
Sai dai a wani bidiyo da ya bazu wanda TheCable ta samu, Sheikh Umar ya musanta zargin, yana cewa ba a tsare shi ba kuma ba a cutar da shi ba.
Malamin ya bayyana cewa an gayyace shi ne kawai domin amsa tambayoyi, ya ba da hadin kai, sannan aka sake shi ba tare da wata matsala ba.
Ya ce:
“Zan yi magana domin gyara rahoton ƙarya da ke yawo, ba a tsare ni ba, an gayyace ni ne kawai, na kuma samu ’yanci”

Source: Original
Shehin malamin ya shawarci magoya bayansa
Sheikh Umar ya bukaci magoya bayansa da mazauna Kaduna su zauna lafiya, su bi doka, tare da guje wa tada hankali ko rikici saboda wannan lamari.
Ya kara da cewa:
“Kada kowa ya dauki doka a hannunsa ko ya haddasa rikici saboda nuna biyayya ga wani”.
Malamin ya kuma bukaci ’yan kasa su bi hanyoyin dimokuradiyya wajen nuna rashin jin dadi, tare da jaddada muhimmancin yin rajista da kada kuri’a.
Ya ce mafita ita ce mutane su zabi shugabanni nagari ta hanyar zabe idan lokaci ya yi, domin inganta shugabanci a kasar.
Obi ya fadi musabbabin talauci a Najeriya
Kun ji cewa tsohon dan takarar shugaban kasa, Peter Obi, ya yi tsokaci kan matsalar muguwar talauci da ake fama da ita a Najeriya.
Peter Obi ya bayyana cewa 'yan Najeriya ne da kansu suka zabi jefa kasar cikin talauci saboda irin abubuwan da suke aikatawa wanda ya jawo matsaloli da dama a kasar
Dan siyasar mai farin jini wajen matasa ya bayyana shawarar da aka ba shi domin ganin an gyara Najeriya yadda ya kamata da kuma sauya gwamnatin APC da ya kira ta da azzaluma.
Asali: Legit.ng

