A Hukumance, Kashim Shettima Zai Karbi Gwamnan da Ya Sauya Sheka zuwa APC

A Hukumance, Kashim Shettima Zai Karbi Gwamnan da Ya Sauya Sheka zuwa APC

  • Mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima zai karbi Gwamna Dauda Lawal zuwa jam'iyyar APC a ranar Talata, 24 ga Maris, 2026
  • Jam'iyyar APC ta kammala shirye-shiryen tarbar mataimakin shugaban kasar aa Zamfara domin halartar taron sauya shekar mai girma gwamna
  • APC ta bukaci ‘ya’yan jam’iyyar a dukkan sassan kananan hukumomin jihqr da su fito kwansu da kwarkwata domin nuna goyon baya

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Zamfara, Abuja - Jam’iyyar APC a jihar Zamfara ta kammala dukkan shirye-shiryen taron karbar Gwamna Dauda Lawal, wanda ya sauya sheka daga PDP zuwa APC.

Ana sa ran Mataimakin Shugaban Kasa, Sanata Kashim Shettima, ne zai jagoranci karbar Gwamna Dauda Lawal zuwa cikin jam’iyyar a ranar Talata, 24 ga watan Maris, 2026.

Kashim Shettima.
Mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima Hoto: @OfficialSKSM
Source: Twitter

Shugaban APC na jihar, Tukur Danfulani Maikatako, ne ya bayyana hakan a ranar Asabar yayin wani taro da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar a Gusau, babban birnin jihar, kamar yadda Arise News ta rahoto.

Kara karanta wannan

Musulmai na shirin karamar Sallah, dakarun NSCDC sun mamaye muhimman wurare a Kano

APC ta yi maraba da Gwamna Lawal

Maikatako ya nuna farin cikin jam’iyyar bisa dawowar Gwamna Lawal APC, yana mai cewa Mataimakin Shugaban Kasa tare da shugabannin jam’iyyar na kasa za su halarci biki.

“Dukkanmu mun san cewa Zamfara ta dade tana daya daga cikin jihohin da APC ke da karfi, kuma gwamnan da ya dawo ya taba zama cikakken dan jam’iyyar a baya," in ji shi.

Ya kara da cewa dawowar gwamnan na nuna ya gamsu da cewa APC ita ce mafita gare shi, yana mai kira ga dukkan ‘ya’yan jam’iyyar su hada kai.

Sakon da APC ta aika ga 'yan jam'iyya

A cewarsa:

“A matsayina na shugaba, ina kira ga dukkan ‘ya’yan jam’iyya a mazabu 147 da ke cikin kananan hukumomi 14 su fito kwansu da kwarkwata domin girmama wannan ziyara ta mataimakin shugaban kasa, wadda za ta kara karfafa APC gabanin zaben 2027.”

Ya kuma bukaci mambobin jam’iyyar su manta da rikice-rikicen cikin gida su hada kai domin ci gaban jihar Zamfara da kasa baki daya.

Kara karanta wannan

Gwamnatin tarayya ta ayyana ranakun hutu don bukukuwan karamar Sallah

Gwamna Dauda Lawal.
Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal Dare a fadr gwamnatinsa Hoto: Dauda Lawal
Source: Facebook

A nasa bangaren, tsohon shugaban APC na jiha Zamfara, Lawal M. Liman, ya bukaci ‘ya’yan jam’iyyar su yada wannan sako a dukkan mazabu da kananan hukumomi, yana mai jaddada cewa APC iyali daya ce da ke aiki domin cimma manufofi guda.

Lawal Liman ya ce hadin kai da goyon bayan juna su ne za su tabbatar da nasarar jam’iyyar APC a zabubbukan gaba, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Matawalle ya yi maraba sa Gwamna Dauda

A wani labarin, kun ji cewa karaminin ministan tsaro, Bello Matawalle ya yaba matakin da Gwamnan Zamfara, Dauda Lawal, ya ɗauka na sauya sheƙa daga PDP zuwa APC mai mulki.

Matawalle ya ce shigan gwamnan APC wani babban tarihi ne a siyasar Zamfara kuma ya yi masa maraba da shiga jam’iyyar.

Ministan ya kara da cewa jihar na bukatar hadin kai domin tinkarar matsalolin tsaro tare da aiwatar da manufofin gwamnatin shugaban kasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262