Ta Zo Gidan Sauki: Tinubu Ya Fadi Abin da Za a Tallashi da Su a Kamfen Zaben 2027
- Shugaban kasa, Bola Tinubu ya yi magana da ba da shawara kan masu tallata shi a zaben 2027 kan abin da za su yi
- Tinubu ya bukaci masu yakin neman zabensa su je kauyuka, kasuwanni da jami’o’i domin bayyana nasarorin gyare-gyaren gwamnatinsa
- Hope Uzodimma da shugabannin APC sun tabbatar da goyon bayansu, suna mai cewa sauyi na bukatar hakuri da jajircewa
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Shugaban kasa, Bola Tinubu, ya yi bayani game da ayyuan alheri da ya gudanar a Najeriya cikin mulkinsa na kusan shekaru 3.
Tinubu ya bayyana sakon da yake so a rika yadawa gabanin zaben 2027, inda ya dorawa jakadun “Renewed Hope” nauyin kai manufofin gwamnatinsa kai tsaye ga ‘yan Najeriya a matakin kasa.

Source: Twitter
Shugaban ya yi wannan jawabi ta bakin Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima, a taron kungiyar gwamnonin APC, cewar Premium Times.
Tinubu ya musanta zargin murkushe yan adawa
Wannan bayani nasa na zuwa ne bayan ya musanta abin da ake yadawa cewa ya kashe jam'iyyun adawa gaba daya a kasar.
Tinubu ya ce ko kadan bai da hannu a rikicewar yan adawa amma kowa yana da damar barin kwale-kwale da ke shirin nitsewa domin tsira.
Hakan bai rasa nasaba da yadda gwamnoni, yan majalisa da sauran yan siyasa ke tururuwa zuwa APC daga jam'iyyunsu.
Tinubu ya ba da shawara kan zaben 2027
Tinubu ya ce bai kamata yakin neman zabe ya takaitu a kafafen sada zumunta ko dakunan taro ba, yana mai cewa:
“Ba a yin zabe a shafukan sada zumunta; ‘yan Najeriya ne ke kada kuri’a.”
Tinubu ya umurci jakadunsa da su fadawa jama’a cewa matsin hauhawar farashi na raguwa, farashin man fetur na sauka, kuma kudin kasa na kara karfi da kwanciyar hankali.
Ya kara da cewa dole ne su yi bayani kan dalilin daukar matakai masu tsauri da yadda za su haifar da ayyukan yi, tsaro, kasuwanci, dama da makoma mai dorewa.

Source: Facebook
Tinubu ya yi kakkausar suka kan yada jita-jita
Shugaban ya kuma bukaci a yaki yada labaran karya da gaskiya, a maye gurbin jita-jita da hujjoji, tare da zama mahadi tsakanin gwamnati da al’umma domin isar da koken jama’a.
Ya bayyana cewa kasafin kudin 2026 na tiriliyan N58.18 zai zama ginshikin sabon matakin bunkasa tattalin arziki, tare da karin kashe kudade a fannin tsaro da manyan ayyuka.
A nasa bangaren, gwamnan Imo kuma shugaban gwamnonin APC, Hope Uzodimma, ya sake jaddada cikakken goyon bayan gwamnonin APC ga manufofin sauyin gwamnatin Tinubu.
Kalaman Tinubu ga sabon shugaban yan sanda
An ji cewa Shugaban kasa Bola Tinubu ya rantsar da Olatunji Disu a matsayin wanda zai jagoranci ragamar rundunar 'yan sandan Najeriya.
Olatunji Disu ya zama sabon mukaddashin Shugaban rundunar 'yan sandan Najeriya bayan nadin da Shugaba Bola Tinubu ya yi masa.
Tinubu ya bukaci Olatunji Disu da ya dawo da zaman lafiya tare da karfafa tsaro a kasar duba da fama da hare-haren yan ta'adda da ake yi.
Asali: Legit.ng

