"Na Yi Nadama": Atiku Ya Bayyana Abin da Ya Sa Shi Cizon Yatsa kan APC
- Tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya, Atiku Abubakar, ya nuna damuwa kan yadda abubuwa suka tabarbare a kasar nan
- Atiku Abubakar ya bayyana cewa abubuwa sun tabarbare fiye da yadda jam'iyyar APC ta tarar da kasar nan bayan hawa madafun iko
- Tsohon mataimakin shugaban Najeriyan ya bayyana cewa dole ne duk wata hadakar siyasa da za a kafa ta kasance mai ma'ana
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya bayyana cewa yana nadamar kasancewa cikin wadanda suka kafa jam’iyyar APC gabanin zaɓen shekarar 2015.
Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana cewa yanayin da kasar take ciki a yanzu ya taɓarɓare fiye da yadda yake kafin samar da jam’iyyar.

Source: Twitter
Jaridar Tribune ta ce Atiku ya yi waɗannan kalaman ne a ranar Alhamis, 26 ga watan Fabrairun 2026 yayin wani taron manema labarai a birnin tarayya Abuja.
Jiga-jigan ’yan adawa sun taru a wajen domin tattauna halin da ƙasa take ciki da kuma sauye-sauyen siyasa da ake yi gabanin zaɓen 2027.
Atiku Abubakar ya tuno da kafa APC
Yayin da yake waiwayar abubuwan da suka kai ga haɗakar jam’iyyun adawa a shekarar 2014, tsohon ɗan takarar shugaban ƙasar ya tuna cewa manyan ’yan siyasa sun haɗa kai ne a ƙarƙashin inuwar APC.
Ya ce sun hadu ne domin ƙalubalantar gwamnatin Shugaba Goodluck Jonathan ta wancan lokacin, saboda damuwar da ake da ita kan rashin tsaro da tabarbarewar tattalin arziƙi.
A cewarsa, haɗakar ta wancan lokacin ta samo asali ne daga fargabar cewa tsarin dimokuraɗiyya yana rauni, kuma ana buƙatar matakan gaggawa domin sauya alkiblar ƙasar, jaridar Vanguard ta kawo labarin.
“Mun haɗu a shekarar 2014 ne saboda mun yi amanna cewa dimokuraɗiyya tana tangal-tangal. Matsalolin lokacin su ne rashin tsaro da tattalin arziƙi. Amma a yau, lamarin ya zama mafi muni fiye da abin da muka yi niyyar gyarawa."
- Atiku Abubakar
Atiku ya koka kan halin da kasa take ciki

Kara karanta wannan
Atiku da jagororin adawa a Najeriya sun cimma matsaya kan sabuwar dokar zabe ta 2026
Atiku ya bayyana cewa halin da ƙasar take ciki a yanzu ya zarce ƙalubalen da suka haifar da kafa APC sama da shekaru 10 da suka gabata, inda ya jaddada cewa dole ne a koyi darasi daga haɗakar siyasa ta baya.

Source: Twitter
Jigon na jam’iyyar ADC ya yi gargaɗin cewa duk wata sabuwar haɗakar jam’iyyu ko tafiyar ’yan adawa dole ne ta kasance mai ma’ana da nufin sake gina dimokuraɗiyya da kuma dawo da amincewar jama’a ga shugabanci.
“Dole ne mu tabbatar da cewa duk wani mataki da za mu ɗauka yanzu burinsa shi ne dawo da ingantacciyar dimokuraɗiyya a Najeriya."
- Atiku Abubakar
Atiku ya yi magana kan tsare El-Rufai
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya nuna damuwa kan ci gaba da tsare Nasir Ahmad El-Rufai.
Atiku Abubakar ya ce za a kama gwamnatin tarayya da alhakin duk wani abu da ya samu tsohon gwamnan na jihar Kaduna.
Tsohon mataimakin shugaban kasar ya jaddada cewa lafiya da jin dadin tsohon gwamnan na da muhimmanci ga iyalansa da abokansa.
Asali: Legit.ng
